logo

HAUSA

Kasar Sin ta samar wa jamhuriyar Nijer wasi motoci kyauta

2022-01-26 11:24:15 CRI

Kasar Sin ta samar wa jamhuriyar Nijer wasi motoci kyauta_fororder_0126-01

A jiya ne, aka gudanar da bikin mika motocin da Sin ta samarwa ofishin kula da hatsi da aikin noma na jamhuriyar Nijer, inda jakadan Sin dake kasar Nijer Jiang Feng, da ministan harkokin cinikayya na kasar Nijer Alkache Alhada, suka halarci bikin tare da gabatar da jawabai.

A cikin jawabinsa, jakada Jiang Feng ya bayyana cewa, Sin tana dora muhimmanci kan hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Nijer a fannin kiyaye tsaron hatsi. Sin za ta tsara shirin farfadowar tattalin arzikin kasa a karo na uku wanda shugaban kasar Nijer Mohamed Bazoum ya gabatar, da aiwatar da ayyuka 9 da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya sanar a wajen taron ministoci karo na 8 na dandalin tattaunawar hadin gwiwar dake tsakanin Sin da Afirka, don taimakawa kasar Nijer wajen tinkarar matsalar karancin hatsi da ake fuskanta a kasar.

A nasa bangaren, minista Alhada ya yi bayani game da yanayin rashin girbin hatsi da tinkarar matsalar karancin hatsi a kasar Nijer a shekarun baya baya nan, kana ya nuna godiya ga gwamnatin kasar Sin da jama’arta bisa ga taimakon hatsi da motoci da ta samar wa jamhuriyar Nijer. Ya kara da cewa, motocin da Sin ta samar a wannan karo za su inganta karfin yin jigilar hatsi da amfanin gona a kasar Nijer. (Zainab)