logo

HAUSA

An kulla yarjejeniyar fitar da tanjarin na kasar Zimbabwe zuwa kasar Sin

2022-01-26 14:09:46 CMG

An kulla yarjejeniyar fitar da tanjarin na kasar Zimbabwe zuwa kasar Sin_fororder_220126-B1-Zimbabwe

A kwanan baya, kasashen Sin da Zimbabwe sun kulla yarjejeniyar fitar da lemun tanjarin na Zimbabwe zuwa kasar ta Sin. A cewar mashawarcin jakadan kasar Sin dake kasar Zimbabwe kan harkokin kasuwanci, mista Zou Xiaoming, wannan yarjejeniyar ta kasance irinta ta farko da aka kulla tsakanin kasashen biyu, wadda za ta karfafa hadin gwiwar Zimbabwe da Sin, musamman ma a bangarorin ciniki, da zuba jari, da aikin gona.

Jami’in ya kara da cewa, “Yarjejeniyar za ta biya bukatun kasar Sin na samun lemun tanjarin, da taimakawa kasar Zimbabwe wajen raya fannin aikin gona, da baiwa manoman kasar damar samun karin kudin shiga, da ma kudin da gwamnatin kasar Zimbabwe take samu. Ban da wannan kuma, takardar yarjejeniyar za ta saukaka aikin zuba jari, ta yadda kamfanonin kasar Sin za su iya zuba karin jari a kasar Zimbabwe a fannonin shuka itatuwan tanjarin, da jigilar lemun tanjarin, da adana su, da samar da takin zamani, da dai sauransu.” (Bello Wang)

Bello