logo

HAUSA

Shawarwari biyar na bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen dake yankin tsakiyar Asiya za su kafa tarihi a sabon zamani

2022-01-26 16:53:39 CRI

Shawarwari biyar na bunkasa hadin gwiwar Sin da kasashen dake yankin tsakiyar Asiya za su kafa tarihi a sabon zamani_fororder_220126-A5-锐评

A ranar 25 ga wata, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya yi muhimmin tsokaci a lokacin da ya jagoranci taron koli ta kafar bidiyo domin murnar cika shekaru 30 da kafuwar huldar diflomasiyya tsakanin kasar Sin da manyan kasashe biyar na tsakiyar Asiya a Beijing. A jawabinsa, shugaba Xi ya gabatar da wasu shawarwari biyar game da yadda za a zurfafa cikakkiyar hadin gwiwa tsakanin bangarorin biyu, inda ake burin karfafa wannan manufa tare da shugabannin kasashen biyar na tsakiyar Asiya. A matsayin wani muhmmin sakamako da aka cimma a taron kolin, bangarorin biyu sun sanar da aniyarsu ta gina tsarin al’ummar Sin da tsakiyar Asiya mai kyakkyawar makoma, tare da bude sabon shafin kyakkyawar hulda a sabon zamani.

Kasashen Kazakhstan, da Kyrgyzstan, da Tajikistan, da Turkmenistan da Uzbekistan su kasance muhimman makwabta dake yamma da kasar Sin. Yau shekaru 30 da suka gabata, kasar Sin ta jagoranci kafa huldar diflomasiyya da wadannan kasashen biyar. Tsakiyar Asiya, shi ne wuri na farko na fara aiwatar da shawarar “ziri daya da hanya daya,” inda aka cimma nasarar kafa huldar dake tsakanin Sin da Kazakhstan karkashin hadin gwiwar cibiyar kan iyakar kasa da kasa ta Horgos, da hadin gwiwar Sin da sansanin sufurin kayayyaki daga tashar ruwa ta Lianyungang dake gabashin kasar Sin zuwa Kazakhstan. An cimma nasarori masu tarin yawa a tarihin hadin gwiwar dake tsakanin Sin da kasashen tsakiyar Asiya.

Sanarwar hadin gwiwar da aka fidda bayan taron kolin ta jaddada cewa, kowace kasa tana da cikakken ’yancin zabar salon ci gabanta da tsarin gudanar da shugabancinta, kana an nuna adawar goyon bayan duk wani nau’in ta’addanci, na kawo baraka, da tsattsauran ra’ayi. Wannan ya  nuna yadda bangarorin biyu ke kokarin dora muhimmanci kan moriyarsu ta bai daya, a fannonin siyasa da tsaro, kana da nuna goyon bayan junansu kan muhimman batutuwan dake shafar moriyarsu. (Ahmad Fagam)