Ruwan Da Ya Duka Ka Shi Ne Ruwa
2022-01-26 16:34:38 CRI
A duk lokacin da aka ambaci gwamnati, abin da zai fadowa jama’a shi ne, matakan da gwamnatin dake mulkin jama’a take dauka na tsaron lafiya da kare mutunci da ma samar musu dukkan abubuwan more rayuwa da dan- Adam ya kamata a ce ya samu karkashin kowa ce irin gwamnati.
Duk gwamnatin da ta mayar da batutuwan da ya shafi moriyar jama’arta a gaban komai, ita ce gwamnati, sabanin yadda wasu kasashe ke amfani da tsarin jagorancin kasashensu, wajen nuna danniya da babakere da cin zali kan sauran kasashe da yankuna, da ma neman kakaba wannan tsarin ala-tilas kan sauran kasashe.
Yadda Jam’iyyar kwaminis mai mulkin kasar Sin a koda yasuhe take mayar da muradun jama’arta a gaban komai, ya sa Sinawa zama a sahun gaba a duniya wajen amincewa da gwamnatinsu, inda wasu alkaluma suka nuna yawan Sinawa da suka tabbatar da amincewa da gwamnatin kasar Sin ya kai kaso 91 bisa dari a shekarar 2021 da ta gabata.
Wannan ya kara tabbatar da manufar gwamnati da JKS mai mulkin kasar Sin na mayar da moriyar jama’a a gaban komai, abin da ya sa jama’ar da ake jagoranta kara nuna yarda da amincewa da ita a dukkan fannoni.
Masu fashin baki dai na cewa, hakan ba abun mamaki ba ne, duba da yadda JKS da gwamnatin Sin ke aiki tukuru wajen cimma muradun al’ummar kasar ba dare ba rana, domin sauke nauyin dake bisa na masu kokarin bautawa jama’arsa.
Sabanin yadda wasu kasashen yamma ke kiran kansu masu rajin kare demokiradiya da jagoranci na-gari, a nata bangaren kasar Sin ta bullo da managartan shirye-shirye da matakai don inganta rayuwar al’ummar da na sauran kasashe dake bukatar tallafi da taimakon kasar Sin a lokacin da suka shiga wani mawuyacin hali, misali na baya-bayan nan shi ne yadda mahukuntar kasar suka gabatar da tallafin jin kai na gaggawa ga tsibirin Tonga, kuma za su ci gaba da mika kudade da kayayyakin bukata domin tallafawa tsibirin gwargwadon bukata, biyowa bayan ibtila’in aman wuta na dutse da ya auku a kasar.
Wannan shi ne shugabanci na gari, ba nuna girman kai da tsoma baki a harkokin cikin sauran kasashe da sunan kare hakkin bil-Adam ko demokiradiya ko wata manufa ta neman cimma mummunar moriya da ta saba dokokin kasa da kasa ba. Matakan da daga karshe ka iya jefa kasashe cikin mawuyacin hali kamar yadda irin hakan ya faru a kasashe irinsu Iraki da Libya da Afghanistan na baya-bayan. (Ibrahim Yaya)