logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon taya murnar ranar Jamhuriya ga takwaransa na kasar Indiya

2022-01-26 20:44:01 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon taya murna ga takwaransa na kasar Indiya Ram Nath Kovind a yau Laraba, inda ya taya Indiya murnar zagayowar ranar da kasar ta cika shekaru 73 da zama jamhuriya.

A wannan ranar ce, shi ma firaministan kasar Sin Li Keqiang ya aike da irin wannan sako na taya murna ga takwaransa na kasar ta Indiya Narendra Modi. (Bilkisu)