logo

HAUSA

Ma’aikatar kasuwanci: Jimillar cinikayyar hajojin kasar Sin ya kai matsayin farko a duniya a shekaru biyar a jere

2022-01-25 12:05:33 CRI

Ma’aikatar kasuwanci: Jimillar cinikayyar hajojin kasar Sin ya kai matsayin farko a duniya a shekaru biyar a jere_fororder_0125-kasuwanci-Ahmad

A safiyar wannan rana, ofishin yada labarai na majalisar gudanarwar jamhuriyar jama’ar kasar Sin ya gabatar da taron manema labarai, inda jami’ai daga ma’aikatar kasuwancin kasar Sin suka gabatar da bayanan harkokin cinikayyar kasar Sin a shekarar 2021. A cewar rahoton, a shekarar 2021, kasar Sin ta zamo kasa ta biyu mafi sayen hajoji a duniya, kana ta zama kasa mafi girma wajen gudanar da hada-hadar cinikayyar kayayyaki a duniya a shekaru biyar a jere, sannan kasa ta biyu mafi samu jarin waje a duniya. Ta kafa yankunan ciniki na gwaji guda 21, da daga matsayin aikin gina tashar ruwa ta cinikayya maras shinge a lardin Hainan. Haka zalika, ta kuma sanya hannu kan yarjejeniyar hadin gwiwar bunkasa tattalin arzikin shiyya (RCEP), wanda ya kasance yarjejeniyar kasuwanci maras shinge mafi girma a duniya. Hada hadar harkokin kasuwancin kasar Sin yana cikin kyakkyawan yanayi, kuma yana kara samun ingantuwa, inda har ma ya zarce hasashen da aka yi. Yawan jimillar kasuwancin waje, da jarin da aka zuba na ketare, da yawan bukatun hajoji gami da jarin da aka zuba a kasashen dake karkashin shawarar “ziri daya da hanya daya” ya kai matsayin koli. (Ahmad)