logo

HAUSA

Sojojin Amurka 7 sun jikkata sakamakon matsalar sauka da jirgin saman yaki samfurin F-35C ya fuskanta

2022-01-25 14:31:24 CRI

Sojojin Amurka 7 sun jikkata sakamakon matsalar sauka da jirgin saman yaki samfurin F-35C ya fuskanta_fororder_0125-U.S.-Saminu

Dakarun sojin Amurka 7 sun jikkata, yayin matsalar sauka da jirgin saman yaki samfurin F-35C ya fuskanta a jiya Litinin a tekun kudancin kasar Sin.

Rundunar sojojin ruwan Amurka ta ce hadarin ya auku ne lokacin da jirgin saman yakin ke kokarin sauka kan jirgin ruwan dakon jiragen yaki samfurin “USS Carl Vinson”, ko da yake matukin jirgin yakin ya tsira.    (Saminu)