logo

HAUSA

MDD ta bukaci a kai zuciya nesa bayan juyin mulki a Burkina Faso

2022-01-25 09:38:24 CRI

MDD ta bukaci a kai zuciya nesa bayan juyin mulki a Burkina Faso_fororder_0125-Burkina-Saminu

Babban magatakardar MDD Antonio Guterres ya yi kira ga sassa masu ruwa da tsaki a siyasar Burkina Faso da su kai zuciya nesa, tare da rungumar tattaunawa, bayan da sojojin kasar masu bore suka yi nasarar juyin mulki a jiya Litinin.

Mr. Guterres ya yi wannan kira ne ta bakin kakakin sa Stephane Dujarric, yana mai Allah wadai da duk wani mataki na kwace iko da karfin makamai. Daga nan sai ya bukaci masu juyin mulkin da su ajiye makamai.

A daya hannu kuma, Mr. Guterres ya bukaci jagororin juyin mulkin da su tabbatar da kare kimar shugaba Roch Kabore, da ma sauran hukumomin gwamnatin kasar.

A jiya Litinin ne dai sojoji masu bore a Burkina Faso suka kwace iko daga gwamnatin Mr. Kabore, kana suka ayyana dakatar da kundin mulkin kasar, da rushe gwamnati da majalissar dokoki, tare da rufe kan iyakokin kasar. (Saminu)