Karin Sinawa na tururuwar shiga gasanni daban daban domin samun karin lafiyar jiki
2022-01-24 09:41:26 CRI
Tun daga kananan shekaru, matasa masu wasan takobi na “fencing”, na nuna karsashin su, yayin da suke kaiwa juna hari da takubban wasan a zauren wasan dake wajen birnin Hefei, fadar mulkin lardin Anhui dake gabashin kasar Sin.
Cikin wadannan matasa, Wu Zhangyi mai shekaru 7 kacal, shi ne karamin su, ya kuma samu horo na kwararru a wannan wasa na tsawon shekara daya da watanni. Wu ya ce "Ina fatan wata rana na shiga gasar Olympics".
Bayan shafe shakaru 4 da bude zauren wasan, yanzu haka kulaf din na da mambobi sama da 150, da koci 3 da suka kai matsayin kasa da kasa, da kuma manyan ‘yan wasan takobin guda 5. Kaza lika akwai kulaflikan wasan fencing daban daban a kusan dukkanin garuruwan gundumomin wannan birni.
Kaso mai yawa na kwararru dake shiga gasannin fencing, da wasan zamiyar kankara na ice hockey, da figure skating, da na harbin kibiya na archery, dukkanin su na karuwa a sassan kasar Sin, ciki har da matasa da kuma dattijai.
Bisa tsarin bunkasa wasannin motsa jiki na shekarar 2021, wanda kasar Sin ta tsara tsakanin shekarun 2021 zuwa 2025, kaso 38.5 bisa dari na al’ummun kasar na kara shiga wasannin motsa jiki na yau da kullum har zuwa shekarar 2025, inda fadin darajar masana’antun wasanni a kasar Sin zai kai kudin kasar tiriliya 5, kwatankwacin dalar Amurka biliyan 785.5.
A watan Yuli na shekarar 2021, Sin ta gabatar da dabarun rage ayyukan gida na dalibai da rubi 2, an kuma rage karin darussa na matasan ‘yan makaranta da akan yi a wajen makaranta, wanda hakan ya kara musu damar shiga harkokin motsa jiki.
Zhang Xue, wanda ke horas da Wu, ya ce wasan fencing baya ga karfafa zuciya da yake yi, yana kuma taimakawa dalibai iya tattara tunanin su, duba da yadda dole sai sun kura ido yayin da suke gudanar da wasan, tare da gwada dabarun da suka koya, da kiyaye dokoki, da nazarin abokan karawa, da kuma daga matsayin bajimtar su kafin su cimma nasara.
Zhang ya kara da cewa, kaiwa matsayin koli na kwarewa a wasan na bukatar yin wasan sau da dama. Duk da cewa ana bukatar kayan wasa na zamani, da horo sosai kafin a iya shiga gasar wasan fencing, karin mutane na shiga neman horo domin hakan.
Alkaluman hukumomi masu ruwa da tsaki sun nuna cewa, a shekarar 2019 da ta gabata, masana’antar wasannin kasar Sin ta kai darajar kudin kasar yuan tiriliyan 3, adadin da ya karu da kaso 10.9 bisa dari idan an kwatanta da shekarar 2018. Kuma ya zuwa karshen shekarar 2020, Sin na da adadin wuraren wasanni sama da miliyan 3.71, wadanda jimillar fadin su ta kai sakwaya mita biliyan 3.
Jin Qiang, tsohon dan wasan damben boxing ne, wanda ke gudanar da dakin wasan a Hefei. Yana kuma cikin masu harkar wasanni da dama dake son fadada damammakin su a kasuwar wasannin yankin. Tun bayan bude wurin wasan na damben Boxing da ya yi a shekarar 2019, Jin ya horas da daruruwan mutane.
Da yake karin haske game da hakan, Jin ya ce "Dalibai na sun kama daga masu shekaru 5 har zuwa shekaru 50, kuma abu ne mai faranta rai ganin yadda wasan ke sauya rayukan su, tare da taimakawa daliban samun karfin jiki, da karin lafiya, kana suna kara rungumar kalubalen rayuwa"