logo

HAUSA

Masanin tattalin arzikin Najeriya ya yi tsokaci kan jawabin shugaba Xi Jinping a wajen taron dandalin tattauna tattalin arzikin duniya

2022-01-24 20:37:17 CRI

Masanin tattalin arzikin Najeriya ya yi tsokaci kan jawabin shugaba Xi Jinping a wajen taron dandalin tattauna tattalin arzikin duniya_fororder_rBABDGAOYbqAKpwxAAAAAAAAAAA207.720x978

Prof. Murtala Sabo Sagagi, malami ne dake koyarwa a makarantar nazarin kasuwanci da sana’o’i wato Dangote Business School dake jami’ar Bayero a jihar Kano, kana masanin tattalin arziki a tarayyar Najeriya.

A zantawar sa da Murtala Zhang, Prof. Sagagi ya yi tsokaci kan muhimmin jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar a wajen taron dandalin tattauna tattalin arzikin kasa da kasa ta kafar bidiyo wanda aka shirya kwanan baya. A cewarsa, kasar Sin tana bada babbar gudummawa wajen farfado da tattalin arzikin duniya da tinkarar matsalar sauyin yanayi, musamman a lokacin da duniya take fuskantar annobar COVID-19 da sauran wasu abubuwa na rashin sanin tabbas.

Prof. Sagagi ya kuma bayyana ra’ayinsa kan maganar tsunduma kasashen Afirka cikin “tarkon bashi” da wasu kasashen yammacin duniya ke ikirarin wai kasar Sin tana yi. (Murtala Zhang)