logo

HAUSA

An kada kuri’u a zaben wakilan kasar Senegal

2022-01-24 11:43:00 CRI

An kada kuri’u a zaben wakilan kasar Senegal_fororder_220124-Fa'iza-Senegal

Da safiyar jiya Lahadi ne aka bude rumfunan zabe a kasar Senegal, domin kada kuri’a a zaben garuruwa da yankunan kasar dake yammacin Afrika.

An kammala kada kuri’ar ne da karfe 6 na yammacin jiyan.

Jimilar ‘yan kasar 6,613,962 ne suka kada kuri’a domin zaben wakilai 3,149 a garuruwa 557 da yankuna 43. An kada kuri’un ne a rumfunan zabe 15,066 dake fadin kasar.

Yayin wadannan zabuka, an samu mutane 250,000 da suka kada kuri’a a karon farko, bayan an yi wa jerin masu zabe garambawul. Hukumar zabe mai zaman kanta ta Senegal, ta samar da masu sa ido 22,00 domin tabbatar da gudanar sahihin zabe. (Fa’iza Mustapha)