Kasar Sin za ta ba Tonga karin agajin gaggawa
2022-01-24 21:18:43 CRI
Mai magana da yawun ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin Zhao Lijian, ya bayyana Litinin din nan cewa, kasar Sin ta yanke shawarar samar da karin rukunonin agajin gaggawa guda uku ga kasar Tonga, sakamakon bala'in aman wuta da tsunami da suka afkawa kasar a baya-bayan nan.
A ranar 19 ga watan Janairu ne, kashi na farko na kayan agajin gaggawa da kasar Sin ta samar suka isa Tonga.