logo

HAUSA

Kamaru: Gobara a gidan rawa ta hallaka mutane a kalla 16

2022-01-24 11:33:16 CRI

Kamaru: Gobara a gidan rawa ta hallaka mutane a kalla 16_fororder_220124-saminu-Kamaru

Ministan ma’aikatar sadarwa na kasar Kamaru Rene Emmanuel Sadi ya ce, wata gobara da ta tashi cikin wani gidan rawa dake birnin Yaounde fadar mulkin kasar, ta hallaka a kalla mutane 16, tare da jikkata wasu mutum 8.

Cikin wata sanarwa da ya fitar, Mr. Sadi ya ce gobarar ta tashi ne da misalin karfe 2:30 na daren ranar Lahadi, a wani gidan rawa mai suna Liv's Night Club Yaouba.

Sanarwar ta kara da cewa, wasu abubuwan wasan wuta da a kan yi amfani da su a gidan rawan ne suka fada kan rufin ginin, wanda hakan ya haifar da wasu fashewa guda 2, inda nan take gobara ta tashi ta kuma cinye rufin ginin. Sanarwar ta ce an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa asibiti.

Shaidun gani da ido sun bayyanawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, akwai sama da mutane 100 a cikin gidan rawar, lokacin da gobarar ta tashi, inda aka samu turmutsutsu yayin da wadanda ke ciki ke kokarin fita, ta kofa daya tilo wadda ta turnike da hayaki.    (Saminu)