logo

HAUSA

An kammala zabukan kananan hukumomin Senegal

2022-01-24 20:40:06 CRI

An kammala zabukan kananan hukumomin Senegal_fororder_9213b07eca806538fc301ecab573664daf34824d

Jiya ne, aka kammala zabukan kananan hukumomi da na yankunan kasar Senegal, yayin da shugaban kasar Senegal Macky Sall da shugabannin siyasar kasar, suka yi kira ga masu zabe, da su kwantar da hankula da kai zuciya nesa bayan kada kuri'unsu.

Shugaba Sall, wanda ya kada kuri'a a Fatick, mahaifarsa da ke tsakiyar kasar Senegal, ya yaba da ingancin tsarin dimokuradiyyar kasar da yadda mutane suka nuna hali na dattaku. 

A wata rumfar zabe da ke Dakar, babban birnin kasar ta Senegal, 'yan jarida sun ga yadda masu kada kuri'a suka yi jerin gwano, domin kada kuri'unsu cikin kwanciyar hankali da lumana. Wasu rumfunan zabe sun kara sa’o’i na kada kuri’a, yayin da masu kada kuri’a a wasu yankunan suka kasa kammala zaben kafin lokacin da aka kayyade, na karfe 6 na yamma, agogon wurin.