logo

HAUSA

Gwamnatin Burkina Faso ta kafa dokar hana fita bayan rikicin kasar

2022-01-24 11:30:30 CRI

Gwamnatin Burkina Faso ta kafa dokar hana fita bayan rikicin kasar_fororder_220124-ahmad-Burkina Faso

Shugaban kasar Burkina Faso, Roch Marc Christian Kabore, ya sanar da kafa dokar takaita zirga-zirga a ranar Lahadi daga karfe 8:00 na yamma zuwa karfe 5:30 na safe, biyo bayan harbe harben da aka samu a barikin sojoji da safiyar ranar Lahadi, kamar yadda dokar fadar shugaban kasar ta amince da daukar matakin.

A wata sanarwar da ofishin ministan ilmin kasar ya fitar ya sanar da rufe makarantun kasar daga yau Litinin zuwa Talata.

An ji karar harbe-harbe da sanyin safiyar ranar Lahadi a barikin sojojin dake Ouagadougou babban birnin kasar, da kuma sauran biranen kasar. Gwamnatin Burkina Faso ta tabbatar da faruwar harbe-harben bindigar sai dai ta musanta bayanan da ake yadawa a shafukan sada zumunta dake nuna cewa sojoji sun kwace iko da kasar.

Ministan tsaron kasar, Barthelemy Simpore, ya bayyana a wani jawabi ta gidan talabijin din kasar cewa, an samu daidaituwar al’amurra a kasar, sai dai ya musanta jita-jitar da ake yadawa cewa sojoji suna tsare da shugaban kasar.

A cewar wasu majiyoyin cikin gidan kasar, daga bisani a wannan rana, masu zanga-zanga sun cinna wuta a helkwatar jam’iyya mai mulkin kasar Burkina Faso dake Ouagadougou. Sannan an samu katsewar hanyoyin sadarwar intanet.

Kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afrika (ECOWAS), ta yi kiran a kwantar da hankula kana ta tabbatar da goyon bayanta ga shugaba Kabore na kasar. (Ahmad)