logo

HAUSA

Lokaci ya yi da ‘yan siyasar Lithuania masu tada hankali za su farka

2022-01-24 19:59:52 cri

Lokaci ya yi da ‘yan siyasar Lithuania masu tada hankali za su farka_fororder_微信图片_20220124190213

Kafofin watsa labaru da dama, ciki har da kamfanin dillancin labaran Reuters sun bayar da rahoton a baya-bayan nan cewa, saboda tashin hankalin dake faruwa a tsakaninta da kasar Sin sakamakon kalubalantar manufar Sin daya tilo da 'yan siyasar kasar Lithuania ke yi, kamfanonin cikin gida na kasar Lithuania da masu zuba jari na kungiyar EU dake kasar sun tabka babbar asara.

Wasu ’yan kasuwa sun yi kiyasin cewa, darajar barnar da aka yi wa kamfanonin gaba daya, ta kai daruruwan miliyoyin Euro. A halin yanzu, kamfanonin suna shan wahalhalu saboda tada hankali da irin wadannan 'yan siyasar kasar Lithuania suka yi. Har ma sun yi korafin cewa, an sadaukar da su ne saboda munanan manufofin gwamnatin kasar, kuma sun bukaci gwamnati da ta gaggauta kyautata alakarta da kasar Sin. Binciken jin ra'ayin jama'a da aka yi a karshen shekarar da ta gabata, ya nuna cewa, amincewar da al'ummar Lithuania ke nunawa kan gwamnatinsu, ta ragu zuwa kashi 17.3 cikin dari. Shugaban hukumar binciken ya bayyana cewa, adadin shi ne mafi kankanta tun bayan kafuwar kasar, wadda ke da alaka da tabarbarewar dangantakar dake tsakanin Lithuania da kasar Sin.

A 'yan kwanakin da suka gabata, majalisar ministocin adawa na kasar Lithuania, ta fitar da wata sanarwa, inda ta amince cewa, Taiwan wani yanki ne da ba za a iya raba shi ba daga kasar Sin, tare da yin kira ga gwamnatin Lithuania da ta gyara kura-kuran da ta yi. Lokaci ya yi da wadancan ‘yan siyasar Lithuania masu tada hankali za su farka! Dole ne su dawo hanyar da ta dace cikin gaggawa, su kuma dauki kwararan matakai don kyautata alaka da kasar Sin, da ba da hujja ga kamfanonin da aka illata da kuma jama'arsu. (Mai fassara: Bilkisu Xin)