Sojojin da suka yi bore na tsare da shugaban Burkina Faso Kabore
2022-01-24 20:09:18 CRI
Rahotanni daga kasar Burkina Faso sun rawaito cewa, wasu sojojin kasar sun tsare shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore a daren jiya a birnin Ouagadougou.
Wata majiyar tsaro da ta bukaci a sakaye sunanta, ta shaidawa kamfanin dillancin labarai na Xinhua cewa, an kai shugaban wani sansanin soji biyo bayan harin da sojojin suka kai.