Ya kamata kasashen yamma su girmama gasannin da suke gudana a sauran kasashe
2022-01-24 21:02:42 CRI
Wasannin motsa jiki wani yanayi dake samar da farin ciki da walwala, da hadin gwiwa ga dan Adam. Sai dai a sakamakon girman kansu, kasashen dake yammacin duniya, su kan gaza fahimtar darajar gasannin wasan motsa jiki da suke gudana a sauran kasashe.
Wani misali dangane da wannan batu, shi ne gasar wasan kwallon kafa ta cin kofin nahiyar Afirka ta AFCON, da ke gudana a kasar Kamaru. Ko da yake ana gudanar da gasar kamar yadda ake bukata, har ma an fara shiga zagaye na biyu na gasar, amma wasu kafofin yada labaru na kasashen yamma, sun fi mai da hankali kan wasu abubuwa marasa kyau game da gasar, irinsu cece-kuce kan yadda aka cire wasu fitattun ‘yan wasa daga kuloflikan kasashen Turai don buga wa kungiyoyin kasashensu gasa, da yiwuwar samun yaduwar cutar COVID-19, da kuskuren da wasu alkalan wasa suka yi, da dai sauransu. Jaridar “the Sun” ta kasar Birtaniya ta wallafa labarin cewa, “karuwar mutane masu kamu da cutar COVID-19 ta kusan hana gudanar gasar AFCON”, wanda kowa ya sani ba gaskiya ba ne.
Yanayin tsaro shi ma ya zama wani abu da kafofin watsa labaru na kasashen yamma suke ta kokarin kambama shi. Jaridar Daily Mail ta kasar Birtaniya ta ce, “an jefa bom cikin dakin karatu, da kai hari kan direba da ‘yan sanda. Yanayin tsaro a kasar Kamaru ya kara tsananta, har ma an yi wa fitattun ‘yan wasan kwallon kafa gargadi cewa, za a iya kai musu hari.” Amma ainihin abun da ya faru shi ne, an samu abkuwar hare-hare a wasu wuraren dake arewacin kasar ne kawai, wadanda kusan ba su yi tasiri sosai kan manyan biranen kasar, da ake gudanar da gasanni ba. Kana a nata bangaren, gwamnatin kasar Kamaru, ta dauki kwararan matakai don tabbatar da tsaro, da kwantar da hankalin mutane masu kallon gasannin.
Hakika yadda aka dora muhimmanci kan wasu abubuwa marasa kyau game da gasar AFCON, ya nuna girman kai na wasu mutanen dake kasashen yamma, da ra’ayinsu na nuna bambancin launin fata. James Yeku wani malami ne dan kasar Najeriya dake aiki a jami’ar Kansas ta kasar Amurka, wanda ya wallafa wani bayani a kwanan baya a shafin yanar gizo na New Frame na kasar Afirka ta Kudu cewa, wasu mutane na kasashen yamma sun nuna damuwa kan gasar AFCON bisa al’adarsu ta nuna kyama. A cewarsa, an kambama yanayin da ake ciki na samun rikici da yaduwar cutar COVID-19 a kasar Kamaru, bisa wani tsohon tunani, wato “nahiyar Afirka wuri ne da ake fama da rikice-rikice da abubuwa masu ban tsoro”.
Wasu mutanen kasashen yamma su ma su kan nuna wani tsohon ra’ayi kan kasar Sin. Misali wasu ‘yan siyasan kasar Amurka, da abokansu, su kan zargi kasar Sin da “keta hakkin dan Adam”, kana bisa wannan dalili ne, sun ce ba za su tura jami’ansu zuwa halartar wasannin Olympics na lokacin hunturu da za su gudana a birnin Beijing na kasar Sin ba, bayan wasu kwanaki 10. Sai dai tunaninsu, da maganarsu, sun sabawa gaskiya. Idan mun dubi yadda kasar Sin ta fid da wasu manoman kasar miliyan 98 da dubu 990 daga kangin talauci, cikin shekarun nan, za mu san kasa ce dake kokarin girmama hakkin dan Adam, da kare shi. Kana wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, tun da aka fara share fagen su, na ta samun goyon baya da amincewa, daga galibin kasashen duniya. A taron ministoci na dandalin hadin gwiwar Sin da Afirka da ya gudana a Dakar na kasar Senegal a watan Nuwamban bara, kasashen nahiyar Afirka sun gabatar da wata hadaddiyar sanarwa, inda suka nuna cikakken goyon baya ga wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing, da kin amincewa da yunkurin siyasantar da batun wasanni. Kana kasar Amurka ma ta yi amai ta lashe, inda ta nema wa wasu jami’anta fiye da 10 izinin shiga kasar Sin, don halartar wasannin Olympics na wannan karo.
Yadda ake gudanar da gasar AFCON cikin nasara, ya sa daukacin al’ummar nahiyar Afirka zama cikin wani yanayi na annashuwa da farin ciki. Kana a kasar Kamaru, tattalin arziki na farfadowa, mutanen kasar sun nuna karin himma da kwazo wajen karbar allurar riga kafin cutar COVID-19, yayin da mutane masu kallon gasanni na kasashen daban daban, su ma suka kulla zumunta mai karfi. A nata bangare, gasar Olympics da za ta gudana a birnin Beijing, ita ma za ta samar da damammaki ga kasashe daban daban domin su kara fahimtar juna, da amincewa da juna, da karfafa zumunta da hadin gwiwa.
Kamata ya yi kasashen yamma su yi watsi da girman kai, da kara girmama ruhin gasannin da ake gudanar da su a sauran kasashe. Ta yadda za a ba wasannin motsa jiki damar taka muhimmiyar rawa a fannin samar da wani yanayi na hadin kai da kaunar juna tsakanin al’ummomin duniya, ta yadda za su iya tinkarar kalobalolin da suke fuskanta cikin nasara. (Bello Wang)