logo

HAUSA

Madagascar na fatan samun cikakkiyar nasarar gasar Olympic ta Beijing

2022-01-23 16:27:34 CRI

Madagascar na fatan samun cikakkiyar nasarar gasar Olympic ta Beijing_fororder_0

Ministan harkokin wajen kasar Madagascar, Patrick Rajoelina, ya bayyana a yammacin ranar Juma’a cewa, kasar Madagascar tana fatan samun cikakkiyar nasarar gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu dake tafe wacce zata gudana a birnin Beijing daga ranar 4 zuwa 20 ga watan Fabrairun wannan shekara.

Cikin sakon bidiyon da ya wallafa a shafin sada zumunta na facebook na ma’aikatar harkokin wajen kasar, Rajoelina yace, Madagascar tana fatan gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing zata samu nasara domin bayar da gudunmawa ga hadin kan kasa da kasa wanda shi ne taken gasar ta Olympic.

Rajoelina ya kara da cewa, wasannin Olympic tamkar wata muhimmiyar hanya ce ta daga matsayin hadin kan kasa da kasa.

Ya ce, ta hanyar mutunta ruhin Olympic, za mu iya cimma nasarar hada mutane wuri guda ta hanyar kyakkyawar fahimtar juna da hadin kan kasa da kasa.

A cewar jami’in diflomasiyyar, ‘yan kasar biyu zasu halarci wannan muhimmiyar gasar wasanni.(Ahmad)