logo

HAUSA

Wasu rukunin makamai da Amurka ke taimakawa Ukraine ya isa Kiev

2022-01-23 17:10:04 cri

Wasu rukunin makamai da Amurka ke taimakawa Ukraine ya isa Kiev_fororder_src=http___nimg.ws.126.net__url=http%3A%2F%2Fdingyue.ws.126.net%2F2022%2F0123%2Faeb19c65j00r65nlv005xc0019000u0m&thumbnail=650x2147483647&quality=80&type=jpg&refer=http___nimg.ws.126

Ma'aikatar tsaron kasar Ukraine ta fitar da sanarwa a jiya Asabar cewa, a wannan rana wasu rukunin makamai da Amurka ta taimaka wa Ukraine ya isa Kiev, babban birnin kasar.

Sanarwar ta ce, wannan shi ne karon farko da aka aika da makamai zuwa kasar Ukraine bisa tsarin taimakon da sojojin Amurka suka yi wa Ukraine na dalar Amurka miliyan 200.

A baya-bayan nan, ana kara samun tabarbarewar dangantaka tsakanin Ukraine da Rasha, inda bangarorin biyu suka jibge jami'an soji da kayan aiki da dama a yankin dake kan iyakarsu. Amurka, Ukraine da NATO sun yi zargin cewa, Rasha ta hada dakaru masu yawa a kusa da iyakar gabashin Ukraine kuma tana yunkurin "kai farmaki" kan Ukraine. Amma, a nata bangaren, Rasha ta musanta zargin, tana mai jaddada cewa, ayyukan kungiyar NATO na barazana ga tsaron kan iyakokin kasar Rasha, kuma Rasha na da hakkin hada sojoji a kan iyakokinta domin kare kasarta.

Ministan harkokin wajen Rasha Sergey Lavrov, ya tattauna da takwaransa na Amurka Antony Blinken a birnin Geneva na kasar Switzerland a ranar 21 ga wata. A wani taron manema labarai da aka kira bayan ganawarsu, Lavrov ya ce, Rasha ba ta da wani shiri na mamaye kasar Ukraine, kuma Amurka da kasashen yamma suna ta zarge-zarge game da rikicin na Ukraine domin su boye yunkurinsu na hada kai da Ukraine a fannin soja, inda kuma suke ci gaba da lalata yanayin tsaron kasar Rasha. (Bilkisu)