logo

HAUSA

Tallafin alluran rigakafi da Sin ta samarwa Jamhuriyyar Congo a karo na uku sun isa kasar

2022-01-22 16:38:14 CRI

Tallafin alluran rigakafi da Sin ta samarwa Jamhuriyyar Congo a karo na uku sun isa kasar_fororder_1000

Tallafin alluran rigakafin cutar numfashi ta COVID-19 da kasar Sin ta samarwa Jamhuriyyar kasar Congo a karo na uku, sun isa birnin Brazzaville, fadar mulkin kasar a daren ranar 20 ga wata, inda aka gudanar da bikin mika alluran. Jakadan kasar Sin dake Jamhuriyyar kasar Congo Ma Fulin, da shugaban babban ofishin ma’aikatar kula da kiwon lafiya ta kasar Congo Jean-Ignace Tendelet, sun je filin jiragen sama domin maraba da zuwan wadannan alluran rigakafi.

Jean-Ignace Tendelet ya godewa gwamnatin kasar Sin, inda ya ce, cikin taron ministocin dandalin tattauna hadin gwiwar Sin da Afirka karo na 8, kasar Sin ta sanar da matakai da dama na taimakawa kasashen Afirka. Ya ce wadannan matakai sun nuna aniyar kasar Sin da ta kasashen Afirka wajen taimakawa juna da hadin gwiwa. Ya ce a halin yanzu kuma, kasar Sin tana ci gaba da samar da tallafin allura ga kasarsa, lamarin da ya nuna muhimmiyar hadin gwiwar dake tsakanin kasashen biyu, da zumunci mai zurfi dake tsakanin al’ummominsu.

A nasa bangare kuma, Ma Fulin ya ce, Jamhuriyyar Congo, muhimmiyar abokiyar hadin gwiwa ce ta kasar Sin a nahiyar Afirka, kuma kasar Sin za ta ci gaba da taimakawa kasar, domin goya mata baya ta fuskar yaki da annobar. (Maryam)