Sinawa mata da suka karo ilmi a ketare sun dawo gida don aiki da zummar taimakawa rayuwar mazauna karkara
2022-01-22 23:54:33 CRI
Mutane da dama na daukar Sinawan da suka yi karatu a kasashen waje a matsayin wadanda suka yi fice a bangarorin karatunsu. Sai dai, da yawa daga cikin wadannan dalibai, ciki har da mata da dama, sun hakura da damarmakin aiki a kasashen waje da suka yi karatu, inda suka dawo gida kasar Sin domin aiki da zummar taimakawa rayuwar mazauna karkara. Ba tare da la’akari da nisan wurin da suka je karatu ba, rayuwar mazauna shi ne abun da suka fi ba da muhimmanci.
Tun daga shekarar 2016, da aka nada ta matsayin babbar sakatariyar kauyen Sunzhuang, wani kauye dake lardin Henan na tsakiyar kasar Sin, Qin Qian, wadda ta dawo daga Australia, take mayar da hankalinta ga kokarin taimakawa mazauna karkarar yaki da talauci.
An haifi Qin Qian ne a shekarar 1986, a birnin Zhumadian na Henan. Tana koyi ne da babanta, wanda ke aiki tukuru, kuma a ko da yaushe, a shirye yake ya taimakawa jama’a.
Qin ta nemi gurbin karatu a sashen nazarin shari’a a jami’ar Yat-sen dake Guangzhou, babban birnin lardin Guandong dake kudancin kasar Sin, yayin jarrabawar neman shiga jami’a ta shekarar 2002. Ta yi fatan zama lauya don ta yi amfani da ilimin wajen taimakawa mutane kare hakkoki da ‘yancinsu.
Bayan ta kammala karatu a jami’ar a shekarar 2006, Qin ta fara karatun neman digiri na biyu a fannin nazarin dokokin kasa da kasa a jami’ar Wollongong dake Australia. Shekaru biyu bayan nan, ta samu shaidar digiri na biyu a bangaren shari’a. Cikin kankanin lokaci, ta dawo kasar Sin. burinta shi ne, aiki a hukumar shari’a domin ta taimakawa mutane masu rauni kare hakkokinsu.
Cikin lokacin kalilan, Qin ta gano cewa, wani gari a Henan na daukar ma’aikata domin aiki a kauyankansa daban-daban. Nan take ta yanke shawarar neman aiki, ta yadda za ta taimakawa mazauna karkara inganta rayuwarsu. Ita ce kadai wadda ta dawo daga ketare da ta nemi aikin a kauye.
“Mutane da dama kan nemi jin dalilin da ya sa na zabi aiki a yankin karkara. Wannan ya sa na yi nazari mai zurfi kan yadda ya kamata mu matasa, mu yi kokarin cimma burinmu a rayuwa,” cewar Qin.
Bayan ta kama aiki a kauyen, Qin ta samu sako daga babanta, inda dattijon ya karfafa mata gwiwar yin aiki tukuru. Wannan ya ba ta karfin kara jajircewa kan aikinta.
A shekarar 2016, kwamitin matasa na JKS na Henan, ya nada Qin a matsayin sakatariyar kauyen Sunzhuang ta farko. Nan take kuma, ta kama aiki. Qin ta taimakawa mazauna kauyen fita daga kangin talauci ta hanyar tallata miyan yaji na Xihua a fadin kasar. Cikin shekarun da suka gabata, Qin ba ta yi kasa a gwiwa ba, wajen kara wayar da kan Sinawa da ma duniya game da wannna miya. Misali, ta yi wa wani tambari mai suna Shamanlou rajista. Ta kuma zabi wani matashi wanda ya koma kauyen Sunzhuang domin fara sana’a, jagorantar mazauna kauyen wajen tallata miyar.
Domin saukakawa mazauna kauyen samun kulawar lafiya, Qin ta inganta kafa tsarin ganin likita ta waya ko bidiyo a Sunzhuang. Inda ya kasance kauye na farko da ya fara amfani da irin wannan tsari a Henan. Ta wannan tsari, likitoci a kauye za su iya tuntubar likitocin dake birane game da wasu cututtuka. A sakamakon haka, mutanen kauye ba sa bukatar yin tafiya mai nisa don ganin likita.
Ta hanyar yin hira da mutane a kauyen, ta gano cewa, akwai bukatar kara kokarin inganta ilimin yara a karkara domin maganin tushen talauci. Bisa kokarin da Qin ta yi, wani kamfani ya bada gudunmuwar kayayyaki da na’urorin zamani na koyarwa ga makarantar Firamare ta Sunzhuang a watan Yunin 2017. Haka zalika, Qin ta karfafawa ‘yan kasuwa daga sassa daban daban na kasar Sin, da su ba da gudunmuwar kudi da tufafi da kayayyakin karatu ga daliban da suka fito daga gidajen talakawa.
A shekarar 2018, yayin da wa’adin aikinta ke dab da karewa, Qin ta yanke shawarar ci gaba da aikin. Yanayin yadda mutanen kauyen ke kallonta ne ya sa ta ci gaba da aikin. Ta gano cewa, mazauna kauyen, wadanda suka dauke ta kamar ‘yar uwarsu, na son ta taimaka musu inganta rayuwarsu.
“Ta hanyar ayyukan da na yi, na gano cewa ya kamata matasa su shigar da akidu da burin kasar Sin cikin rayuwarsu. Ya kamata su aiwatar da abun da suka koya ta hanyar taimakawa mazauna kauye tserewa talauci. Ta wannan hanya, matasa za su iya cimma manufarsu a rayuwa,” cewar Qin.
Peng Yang, ‘yar asalin Fengjie, wata gunduma a birnin Chongqing na kudu maso yammacin kasar Sin, ta yi fice a shekarun baya-bayan nan. Ko mene ne dalili? Ta nuna a aikace, yadda mutum zai iya cimma burinsa da bin abun da yake zuciyarsa.
Peng ta ba mutane da dama mamaki, ciki har da kawaye da ‘yan uwanta, a lokacin da ta yanke shawarar barin aikin dake da albashi mai kyau, a matsayin ma’aikaciyar bankin zuba jari na Ingila, domin dawowa gida ta fara nata kasuwanci. Ta yanke shawarar ne jim kadan bayan ta kammala karatun digirin digirgir a jami’ar Cambridge a fannin nazarin tattalin arziki. Tana daya daga cikin daliban jami’ar masu hazaka a lokacin da take karatu daga shekarar 2007 zuwa 2016.
Labarin Peng Yang na jagorantar manoman Fengjie wajen yaki da talauci ta hanyar noman lemu, ya bayyana ne lokacin wani taron nune-nunen nasarorin da Sin ta samu wajen yaki da talauci, da aka yi wa taken “Cimma burin samun kyautatuwar rayuwa”. An yi nune-nunen ne a watan Yunin 2018 a hedkwatar MDD dake New York. Zaunnanen ofsihin tawagar kasar Sin a majalisar ne ya dauki nauyin taron.
Peng ba za ta taba mantawa da lokacin da ta ji taken kasar Sin a karon farko ba a lokacin wani taron, wato tun bayan da ta fara karatu a jami’ar Cambridge. Wato a watan Yunin 2014 ne, a ranar ne Firaminsitan kasar Sin Li Keqiang, yayin ziyararsa a Birtaniya, ya gana da Peng tare da sauran daliban kasar Sin masu hazaka dake Birtaniya. Peng ta kuduri niyyar dawowa gida ta yi aiki domin taimakawa ‘yan uwanta Sinawa.
Yayin da take nazari domin samun kyakkyawar dabarar taimakawa mutane a garinsu wajen samun kudi, Peng ta tuna lokacin da take karatu a Cambridge. A lokacin da take karatun bayan digiri a jami’ar, Peng tare da malaminta, sun rubuta wata mukala kan yadda za a inganta habakar tattalin arziki da rage talauci a Chongqing.
Daga nan, ta shirya taimakawa talakawan dake Fengjie inganta rayuwarsu ta hanyar abun da ta koya daga jami’ar Cambridge, wato ta hanyar samarwa da kuma tafiyar da nata kasuwanci.
Daga baya, Peng ta yanke shawarar taimakawa manoman Fengjie samun wadata ta hanyar karfafa musu gwiwar noman lemu. Wannan kayan marmari mai zaki ne ke tunatar da ita da gidanta a lokacin da take jami’a.
A lokacin rani na shekarar 2016, jim kaddan bayan dawowarta, Peng ta kafa kamfanin Chongqing Anyijia. Ta kuma yi wa lemun da kamfaninta ke sayarwa rajista da tambari mai suna So Orange, ta yadda za ta samu saukin fadada kasuwancinta.
Cikin kankanin lokaci da kafa kamfanin, ta sayo wata na’ura ta auna adadin zaki da tsamin lemu. Wannan na’ura, ita ce irinta ta farko a Chongqing.
Da farko, galibin ma’aikatan dake aikin kunshe lemu a kamfaninta, ba su fahimci dalilin da ya sa ake rarraba lemun ba. Peng kan jagoranci ma’aikatan sashen cinikayya wajen rarraba lemun. “kamfanin kan yi bikin murnar haihuwar ma’aikata a kowanne wata,” cewar Peng. “da ma’aikatan suka fahimce mu, sai suka fahimci dalilin da ya sa muke bada muhimmanci sosai ga ingancin kayayyakinmu.”
A koda yaushe, Peng ta kan bullo da kyawawan dabaru yayin da take tafiyar da kasuwancinta. Misali, ta dauki wani mai zane domin ya zana kowanne ma’aikaci dake aikin rarraba lemu a kamfanin, ta yadda masu saye za su gane wadanda ke kunshe musu lemu, ta hanyar zanen da aka lika a jikin kwalayen lemun.
Peng ta kuma jagoranci masu tsara fasali na kamfanin wajen kirkiro wani kunshi irin na bayarwa kyauta, wanda ke dauke da manyan lemu 6 a matsayin iyaye, sai kuma wasu kanana 6, a matsayin ‘ya’yansu. Wannan ya samu karbuwa sosai a wajen kwastomomi.
Bayan sun samu labarin ci gaban kamfanin Anyijia, da yawa daga cikin mazauna Fengjie, ciki har da mata da dama da suka bar gida, sun koma garinsu don yi wa kamfanin aiki.
Kwalliya ta biya kudin sabulu, game da kokarin Peng da ma’aikatanta, inda So Orange ya zama daya daga cikin ayyukan gona na zamani da ya yi fice, haka kuma daya daga cikin manyan tambura 10 na kasar Sin.
“Yayin da kasar Sin ta yi namijin kokari wajen inganta dabarun farfado da yankunan karkara cikin shekarun da suka gabata, ni ma na shigar da tawa dabara, ta samar da kamfanin zamani a kauye, domin cimma burin kasar Sin,” cewar Peng Yang.