logo

HAUSA

Jami’in AU: Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta samarwa Afrika damarmakin ci gaba

2022-01-22 15:44:55 CRI

Jami’in AU: Shawarar Ziri Daya da Hanya Daya ta samarwa Afrika damarmakin ci gaba_fororder_Albert Muchanga

An bayyana shawarar Ziri Daya da Hanya Daya da aka gina bisa tushen moriyar juna, a matsayin wadda ta samarwa nahiyar Afrika damarmakin ci gaba.

Kwamishinan cinikayya da masana’antu na hukumar kula da Tarayyar Afrika AU, Albert Muchanga ne ya bayyana haka, lokacin da yake tattaunawa da kamfanin dillancin labarai na Xinhua, inda ya jaddada cewa, adadin kasashen Afrika da yanzu ke aiwatar da shawarar na karuwa, kuma shawarar ta ingiza ci gaba a fadin nahiyar.

A cewarsa, hakika, shawarar Ziri Daya da Hanya Daya na samar da damarmakin ci gaban ababen more rayuwa, ciki har da makamashi da inganta tituna, kuma ‘yan Afrika na maraba da ita.

Ya ce a baya-bayan nan ne aka rattaba hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna tsakanin AU da hukumar raya kasa da gyare-gyare ta kasar Sin, karkashin hadin gwiwar AU da kasar Sin kan shawarar Ziri Daya da Hanya Daya, wadda ta shafi bangarorin lafiya da abinci da tsaro da ababen more rayuwa da makamashi.

Ya kara da cewa, an samar da yarjejeniyar ce bisa moriyar juna, kuma za ta amfanawa abokan huldar biyu, wato nahiyar Afrika da kasar Sin.

Bugu da kari, ya ce ta hanyar rattaba hannun, sun bayyana nufinsu na cewa sun shirya, kuma sun kuduri aniyar aiwatar da yarjejeniyar. (Fa’iza Mustapha)