logo

HAUSA

Tabani Gunye: Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing za ta nuna salon kasar Sin ga duniya

2022-01-21 09:43:13 CRI

Tabani Gunye: Gasar Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing za ta nuna salon kasar Sin ga duniya_fororder_0121-i01-President of Zimbabwe Olympic Committee

Jiya ne, shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasar Zimbabwe Thabani Gonye Thabani GONYE, ya bayyana fata da imaninsa cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing za ta gudana cikin nasara.

A wata hirar da ya yi da wakilin babban gidan rediyo da talabijin na kasar Sin (CMG), Tabani Gunye ya yi kakkausar suka kan yadda ake siyasantar da harkokin wasanni. Yana mai cewa, ba za a iya hada wasanni da siyasa ba. Wasannin Olympics wani lokaci ne dake hada kan jama'a daga sassa daban-daban na duniya, kuma gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing, za ta nuna wa duniya irin salon kasar Sin. Yana mai cewa, "Jama'ar kasar Sin sun yi aiki mai kyau. Kun shirya, kuma za ku nuna wa duniya yadda kasar Sin take. Jama'ar kasar Sin, za su gabatarwa duniya wani kasaitaccen bikin Olympics, kuma suna maraba da duniya ta ji dadin wasannin na Olympics. Akwai abubuwa da dama da zan tuna game da Beijing. Kokarinku ba zai bi ruwa ba, kuma duk wani aiki tukuru da aka yi a shekarun baya, zai samar da sakamako yayin da aka samu nasarar gudanar da gasar Olympics ta lokacin sanyi ta shekarar 2022 a nan birnin Beijing. Ina yi muku fatan alheri da samun nasara!" (Ibrahim Yaya)