logo

HAUSA

Dole ne Amurka ta daina zaluncin siyasa ga masanan kimiyya ‘yan asalin kasar Sin

2022-01-21 20:46:45 CRI

Dole ne Amurka ta daina zaluncin siyasa ga masanan kimiyya ‘yan asalin kasar Sin_fororder_Amurka

Jiya Alhamis 20 ga wata, agogon Amurka, hukumar shari’a ta kasar ta soke karar da aka kai Chen Gang, farfesa a kwalejin MIT ‘dan asalin kasar Sin a hukumance, daga baya Chen Gang ya fitar da wata sanarwa, inda ya bayyana cewa, ya shiga yanayi na jin tsoro matuka a cikin shekarar da ta gabata.

An kama shi a gidansa dake jihar Massachusetts a watan Janairun bara, saboda zargin wai bai fayyace alakar dake tsakaninsa da wata jami’ar kasar Sin yayin da yake neman kudin aiki daga ma’aikatar makamashin kasar Amurka ba. Sai dai kuma lamarin ba haka yake ba, domin kuwa shugaban kwalejin MIT Rafael Reif, shi ma ya fitar da wata wasika a fili, inda ya shaida cewa, kwalejin MIT ce ta gudanar da hadin gwiwa da jami’ar kasar Sin.

Hakika a cikin ‘yan shekarun da suka gabata, gwamnatin Amurka tana gurgunta cudanyar al’adu da kimiyya da fasaha dake tsakanin kasashen Sin da Amurka, sakamakon yunkurinta na hana ci gaban kasar Sin.

Abun ban mamaki ne a ga al’amurra irin wadannan suna faruwa a kasar Amurka, wadda take kiran kanta kasa mafi rinjaye wajen gudanar da harkokin kasa bisa tsarin demokuraidya da dokoki. (Jamila)