logo

HAUSA

Moussa Faki Mahamat: Bazuwar cutar COVID-19 ya haskaka raunin tsarin kiwon lafiyar Afirka

2022-01-21 19:33:20 CRI

Moussa Faki Mahamat: Bazuwar cutar COVID-19 ya haskaka raunin tsarin kiwon lafiyar Afirka_fororder_00

Shugaban hukumar zartaswar kungiyar tarayyar Afirka ta AU Moussa Faki Mahamat, ya ce yanayin bazuwar cutar COVID-19 a kasashen Afirka, ya kara haskaka raunin tsarin kiwon lafiyar nahiyar.

Moussa Faki Mahamat, wanda ya bayyana hakan jiya Alhamis, cikin jawabin sa a taron yini 2, na mambobin kwamitin wakilan dindindin na kungiyar AU ko PRC a takaice, ya kuma shaidawa wakilan kasashen nahiyar cewa, ya dace kasashen da suke wakilta, su yi la’akari da hanyoyin sake inganta tsarin kiwon lafiya a Afirka. Ya ce irin muhimmancin da za a dora kan tsara ayyukan cibiyar yaki da cututtuka ta Afirka ko Africa CDC, da hadin gwiwa wajen samar da alluran rigakafi, da aikin tabbatar da kafuwar cibiyar ilimin likitanci ta Afirka, dukkanin su za su taka rawar gani, wajen fitar da nahiyar daga kangin kalubalen kiwon lafiya.

PRC ta shirya taron na yini 2 na bana, bisa taken “Gina tsari mai karfi game da samar da abinci mai gina jiki: Ingiza tasirin al’umma da bunkasa tattalin arziki”, ya kuma gudana a ranekun Alhamis da Juma’ar nan.    (Saminu)