Matasan Taiwan dake neman tushensu a babban yankin kasar Sin
2022-01-20 11:01:20 cri
"Mutum kamar bishiya yake, wato dai idan ya samu 'tushen' zai yi girma yadda ya kamata. Mutumin da ba shi da ‘tushe’, zai kasance kamar ciyawar agwagwa ne." Bayan kusan shekaru 30 tana zama da aiki a babban yankin kasar Sin, ‘yar kasuwa da ta fito daga yankin Taiwan na kasar mai suna Jiang Peiqi ta yi sa'a cewa, ta sami "tushen" a gundumar Lianjiang dake babban yankin kasar.
A shekarar 1992, Jiang Peiqi ta bi mahaifinta zuwa gundumar Lianjiang da ke lardin Fujian, dake bakin teku a kudu maso gabashin kasar Sin. A yayin shagalin murnar bikin bazara na gargajiyar kasar da aka shirya a waccan shekarar, mawaka daga babban yankin kasar Sin, da Hong Kong, da Taiwan sun rera wata waka tare, inda aka rera kamar haka, "Allah ya taimake ku wajen cimma babban buri a fannonin aiki da iyali, da fatan za ku iya samun sakamako mai kyau bisa kokarin da kuka yi."
Jimlar “Za ku iya samun sakamako mai kyau bisa kokarin da kuka yi” ta nuna yaddda Jiang Peiqi da mahaifinta suka raya sana’arsu a babban yankin kasar Sin. Jiang Peiqi ta ce, bakarara ce ake iya samu a ko ina a wancan lokacin, kuma babu inda ko da za a sauka daga mota. Amma, yanzu ciyayi sun mamaye wannan yanki, kuma manyan gine-gine da aka gina daya bayan daya, sun soma tasowa daga kasa suna ta kyautata halin da gundumar ta Lianjiang ke ciki.
Babban abin alfahari ne ga Jiang Peiqi, da ta shaida da kuma shiga cikin yunkurin sauye-sauye na garinsu.
A shekarar 1992, mahaifin Jiang Peiqi, ya yanke shawarar gina filin wasan golf a gundumar Lianjiang, aikin da ya shafe tsawon lokaci. A cikin shekaru 6 da suka gabata, an cika wurin da kasa har kimanin miliyoyin cubic meters, kuma an gina madatsar ruwa mai tsawon kilomita 3.3, kana an shuka dubun-dubatar tsirrai.
A ganin Jiang Peiqi, dalilin da yasa mahaifinta ya dage kan wannan aiki, shi ne ra’ayin da yake tsayawa a kai wato "tushe". Mahaifinta ya kan ce, a lokacin yarintar sa, yana son yanayin zafi sosai, saboda a wannan lokacin, a kan yi ambaliyar ruwa, ta yadda yara ba za su iya tafiya makaranta domin karatu ba, sai dai yin wasa a gida, su sauke lallausan kofa su yi amfani da su a matsayin jiragen ruwa. Ko da yake wannan abin wasa ne, amma gaskiya ya nuna mawuyacin halin da mazauna wurin suke ciki. Jiang Peiqi ta ce, bayan an kammala aikin gina madatsar ruwan, mazauna kauyen Lianjiang sun yi bankwana da irin halin zaman rayuwarsu da na.
Bayan rasuwar mahaifinta, Jiang Peiqi, wadda ta kira kanta "'yar gundumar Lianjiang" ta zabi ci gaba da yin gwagwarmaya kan aikin mahaifinta.
A halin yanzu, Jiang Peiqi tana kokarin raya wannan filin wasan golf, a matsayin cibiyar horar da kwararru a fannin kiwon lafiya, da kuma cibiyar bincike ta kiwon lafiya ta babban yankin kasar Sin, da yankin Taiwan, tana fatan lambun muhallin hallitu da ta gada daga mahaifinta zai ci gaba da amfanar mazauna wurin.
Jiang Peiqi ta ce,“Yanzu yawancin matasa a Taiwan sun rude saboda ba su da ra’ayin ‘tushe’.” A ganinta, idan mutum bai san inda ya fito ba, to ba zai san inda zai dosa ba.
Bangarorin biyu na mashigin Taiwan suna da asali iri daya, harshe daya da al’adu iri daya. A cikin 'yan shekarun nan, da yawa daga cikin matasan Taiwan da suka soma aiki, da zama a babban yankin kasa, sun samu “tushe” a nan, kuma sun tabbatar da burinsu na gwagwarmaya. Wasu daga cikinsu suna samun jin dadin zama a garin kaka da kakaninsu, yayin da wasu ke samun karfi daga “tushensu” kuma suna gano sabbin damammaki.
A yayin taron mashigin teku na Taiwan karo na 13 da aka gudanar, an nada Huang Kaijia, "Tauraron Kasuwanci" na matasan Taiwan a lardin Fujian a shekarar 2021. Ta halarci taron sanye da doguwar riga ta musamman. Ta gaya mana cewa, wannan ita ce hanyarta ta yada al'adun gargajiyar kasar Sin. Ta kara da cewa, matasan Taiwan ba su fahimci kan babban yankin kasar Sin sosai ba, don haka, tana fatan gaya wa mutanen Taiwan, musamman matasa, wani ainhin babban yankin kasar ta hanyar kokarinta.
Kamfanin yin kirkire-kirkire kan al'adu da Huang Kaijia ta kafa a halin yanzu, yana amfani da sabbin kafofin watsa labaru don ba da labaran da suka shafi da al'adun jama'ar wuraren biyu. Ita kanta sau da yawa tana shiga cikin ayyukan nazarin al'adu na kakanni dake wuraren biyu.
A watan Yuni na shekarar da ta gabata, lokacin da ta ga rawayen kogin a karon farko, ta kuma dawo da ruwan dake cikin wannan kogin Uwar na musamman zuwa Taiwan. A cewarta, ko da yake ba ta iya jin muryar gudun ruwan rawayen kogin, amma tana iya kaunar kasar uwa ta ruwan da ta tara.
Tabbatar da “tushe” na nufin tabbatar da burin da za a cimma a nan gaba. 'Yan kasuwa matasa na Taiwan suna amfani da nasu labaran, don bayyana tsayawarsu kan abin tunawa na bai daya na duk al’ummar kasar Sin, da kuma tushen ruhaniya na al'ummar. Irin wannan karfin da aka samu daga kauna, yana sanya zukatan ’yan uwa na bangarorin biyu, wato babban yankin kasar Sin da na Taiwan su kasance da alaka sosai.