logo

HAUSA

Yanayin da Amurka ke ciki sakamako ne na gazawar dimokaradiyyar kasar

2022-01-20 21:17:14 CRI

Yanayin da Amurka ke ciki sakamako ne na gazawar dimokaradiyyar kasar_fororder_amurka

Shekara guda da ta gabata, wato ranar 20 ga watan Janairun bara, shugabannin Amurka suka yi alkawari a yayin shan rantsuwar kama aiki cewa, za su shawo kan annobar COVID-19, tare da hada kan Amurkawa. To sai dai kuma a yau, shekara guda bayan wancan alkawari, cutar ta kara bazuwa tsakanin al’ummar kasar, inda mummunan tasirin ta ya kara tsananta a sassan kasar.

Wannan sakamako, na nuni ga yadda kalaman shugabannin Amurka kan zama tamkar wata farfaganda, da su kan yi a duk lokacin da suke shan rantsuwar kama aiki, kuma abu ne mai wahala su iya cika alkawuran da suke yiwa jama’ar su.

Sakamakon wani binciken jin ra’ayin jama’a na baya bayan nan ma ya nuna cewa, karbuwar jagororin Amurka ga al’ummar kasar, ta ragu zuwa kaso 40 bisa dari, daga kaso 57 bisa dari a shekara guda da ta gabata, lokacin da sabuwar gwamnatin kasar ta kama aiki.

Masharhanta na cewa, hadakar arziki da karfin iko na iya haifar da mulkin da ‘yan tsiraru ke sarrafa shi, wanda kuma ke karya kashin bayan dimokaradiyya. Wannan dai shaida ce dake nuna salon siyasar Amurka ya gaza.  (Saminu)