logo

HAUSA

An bude filin wasa na zamani da kamfanin kasar Sin ya gina a Kongo DRC

2022-01-20 11:04:17 CRI

An bude filin wasa na zamani da kamfanin kasar Sin ya gina a Kongo DRC_fororder_220120-A1-DRCONGO

A ranar Laraba an bude katafaren filin wasa na zamani irinsa na farko da kamfanin Sinohydro 2 na kasar Sin ya gina a garin Goma, birni mafi girma dake shiyyar arewa maso gabashin demokaradiyyar Kongo DRC.

Sabon filin wasan, wanda aka fara aikin gina shi tun a shekarar 2017 a birnin Goma, babban birnin lardin North Kivu a DRC, yanzu haka an bude filin wasan bayan kammala ayyukan shimfida koriyar ciyawa da sauran muhimman kayayyaki a cikin filin.

Aikin wanda kamfanin kasar Sin ya samar da kudaden gudanar da shi karkashin shirin hadin gwiwa na kasar Sin da Kongo (ACGT), filin wasan yana dauke da kujerun zama 15,000, ya baiwa birnin Goma damar samun filin taro na zamani irinsa na farko wanda ya dace da karbar tarukan kasa da kasa.

Bayan kammala aikin wanda kamfanin kasar Sin ya gina, Romy Ekuka Lipopo, mataimakin gwamnan lardin North Kivu, ya bayyana filin taron a matsayin kaya mai daraja, ya ce zai baiwa lardin na North Kivu damar karbar muhimman wasanni a nan gaba. (Ahmad Fagam)