logo

HAUSA

Duniya Na Jinjinawa Sin Bisa Shirya Gasar Olympics Duk Da Kalubalen Da Ake Fuskanta

2022-01-20 16:22:17 CRI

Duniya Na Jinjinawa Sin Bisa Shirya Gasar Olympics Duk Da Kalubalen Da Ake Fuskanta_fororder_220120-Sharhi-Saminu-hoto

Har yanzu, sassan kasa da kasa na ci gaba da bayyana fatan alheri ga gasar Olympics ta lokacin hunturu da birnin Beijing ke daf da karbar bakuncin ta, duk da kalubalen da duniya ke fuskanta ta fannoni daban daban.

Yayin da duniya ke shan fama da kalubalen yaduwar annobar COVID-19, da tafiyar hawainiya a fannin farfadowar tattalin arziki, da sauran matsaloli masu ciwa duniya tuwo a kwarya, a hannu guda, kasar Sin ta tunkari shirya wannan gasa mai muhimmanci yadda ya kamata, kuma bisa lokacin da aka tsara gudanar da ita.

Masharhanta da dama sun jinjinawa kasar Sin, bisa tsara nagartattun manufofin gudanar da wannan gasa, wanda hakan ya sa wasu ke cewa, Sin din ta tabbatar da ruhin bil-adama maras iyaka. Musamman kasancewar gasar za ta tattaro al’ummu daga sassan duniya daban daban, kamar daga ’yan wasa, da masu rakiyar su, da jami’ai, a kuma gabar da Sin din ta tanadi matakai daban daban na amfani da na’urori, da dabarun zamani na tabbatar da tsaron lafiyar kowa da kowa.

Ko shakka ba bu, kammalar wannan gasa cikin nasara, zai sanya Sin zama zakaran gwajin dafi, dake taka muhimmiyar rawa wajen tabbatar da mafarkin bil adama na tunkarar dukkanin kalubale tare da cimma nasara.

Har ila yau, nasarar gudanar wannan kasaitacciyar gasa a wannan lokaci, zai faranta ran al’ummun duniya, da karawa jama’a kwarin gwiwar farfadowa bayan haye wahalhalu na tattalin arziki da zamantakewa a matakin kasa da kasa. Baya ga sada zumunci da hadin kai, da yaukaka abota da gasar za ta haifar tsakanin kasashe daban daban. (Saminu Hassan)