logo

HAUSA

Xi Jinping ya aike da sakon ta'aziyya ga Sarki Tupuo VI na Tonga kan mummunan bala'in da dutsen Tonga ya haddasa

2022-01-20 10:26:56 CRI

Xi Jinping ya aike da sakon ta'aziyya ga Sarki Tupuo VI na Tonga kan mummunan bala'in da dutsen Tonga ya haddasa_fororder_220120-I1-Tonga

Jiya ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya aike da sakon ta'aziyya ga sarki Tupou na 6 na kasar Tonga bisa mummunan bala'in da amon wutan da dutsen Tonga ya haifar.

Xi Jinping ya ce, ya kadu matuka da ya samu labarin cewa, dutsen Tonga ya yi amon wuta tare da haddasa bala'in tsunami da wasu munanan bala'o'i, wanda ya haddasa hasara mai dimbin yawa. Shugaba Xi ya ce, a madadin gwamnati da jama'ar kasar Sin, da shi kainsa, ya mika sakon ta'aziyya ga gwamnati da jama'ar kasar Tonga. Sin da Tonga manyan abokan hulda ne bisa manyan tsare-tsare da ke goyon baya da taimakawa juna.

Ya kara da cewa, bangaren kasar Sin yana son bayar da tallafi gwargwadon karfinsa ga bangaren tsibirin Tonga don taimakawa al'ummar Tonga shawo kan bala'in da suka fuskanta da kuma sake gina kasarsu ta asali.

A wannan rana, shi ma firaministan kasar Li Keqiang ya aike da sakon ta'aziyya ga takwaransa na kasar Tonga Sovaleini. (Ibrahim)