logo

HAUSA

MDD na kokarin samun izinin tashin jiragen samanta a Mali

2022-01-19 10:58:00 CRI

MDD na kokarin samun izinin tashin jiragen samanta a Mali_fororder_220119-yaya2-Mali

Stephane Dujarric, kakakin babban sakataren MDD Antonio Guterres ya bayyana cewa, majalisar tana kokarin ganin an ba da izinin zirga-zirgar jiragen sama a kasar Mali, a daidai lokacin da hukumomin kasar suka bullo da sabbin matakai.

Kakakin ya ce, hukumomin kasar ta Mali, sun sanyawa majalisar wasu sabbin ka’idodji, kafin jiragen samar majalisar su samu izni. Yana mai cewa, yanzu haka an dakatar da tashin dukkan jirage, a gabar da MDD ke kokarin samun karin haske game da wadannan matakai. Ganin yadda matakan suka kawo cikas matuka ga kokarin majalisar na gudanar da ayyukanta yadda ya kamata. Don haka, a cewarsa, suna ci gaba da tattaunawa da hukumomin kasar ta Mali.

Ya ce, sabbin dokokin ba su yi tasiri kan jiragen sama na “medevac” ko na gaggawa na MDDr ba, wacce ke da rundunar kiyaye zaman lafiya a Mali.

A cewar Dujarric, abubuwan da ake bukata game da samun izinin tashin jiragen, yana bisa turba, kuma haka lamarin yake, saboda kasa mai ’yanci ce take da iko kan sararin samaniyarta. Sai dai ba zai ce uffan ba, kan lokaci da kuma dalilin da ya sa aka sanya sabbin ka'idojin. (Ibrahim Yaya)