logo

HAUSA

Shugaban Najeriya: Najeriya ta samu karuwar noman shinkafa

2022-01-19 09:59:48 CRI

Shugaban Najeriya: Najeriya ta samu karuwar noman shinkafa_fororder_220119-Ibrahim-Shinkafar Nigeria

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari, ya bayyana jiya Talata cewa, noman shinkafa a kasar ya karu zuwa sama da tan miliyan 7.5 a duk shekara, wanda hakan ya yi matukar karuwa daga matsakaicin yawan shinkafar da ake samarwa, na kasa da tan miliyan hudu cikin kimanin shekaru 22.

Buhari ya bayyana hakan ne a Abuja, babban birnin kasar, a lokacin da yake jawabi a yayin bikin kaddamar da dalar shinkafa da aka yiwa lakabi da “sky high rice paddy” wanda babban bankin Najeriyar wato CBN ya shirya.

Shugaban na Najeriya ya bukaci ’yan Najeriya, da su yi hakuri saboda yadda ake noman abinci a kasar, musamman fadada noman shinkafa, zai rage farashin kayan abinci, ta yadda hakan zai sa kowa ya samu abinci cikin sauki.

Ya kara da cewa, a fadin Najeriya sama da kananan manoma miliyan 4.8 ne, suka samu tallafi daga shirin Anchor Borrowers’ Programme (ABP), wani shiri da babban bankin kasar na CBN ke tallafa wa manoman kasar, domin kara samar da kayayyakin amfanin gona guda 23 da suka hada da masara,da shinkafa, da kwarar manja, da koko, da auduga, da rogo, da tumatir, da dabbobi.

Shugaba Buhari ya ce, karkashin shirin na ABP wanda gwamnatinsa ta kaddamar, yanzu Najeriya na da sama da ingantattun masana'antun sarrafa shinkafa guda 50, wadanda za su samar da guraben ayyukan yi, da rage zaman kashe wando, inda ya kara da cewa, za a samu karin sakamako, da zarar irin wadannan sabbin masana'antu biyu a Legas, cibiyar tattalin arzikin kasar, gami da Katsina a yankin arewa maso yammancin kasar suka fara aiki. (Ibrahim Yaya)