logo

HAUSA

Me ya sa Amurkawa ke kara nuna rashin gamsuwa da gwamnatin kasarsu?

2022-01-19 21:15:09 CRI

Me ya sa Amurkawa ke kara nuna rashin gamsuwa da gwamnatin kasarsu?_fororder_amurka

Cibiyar Edelman, wadda ita ce mafi girma a duniya a fannin nazarin huldar al’umma, ta fitar da rahoton ta na bana, mai taken "Edelman Trust Barometer". Rahoton wanda cibiyar ta fitar a jiya Talata, ya nuna yadda Amurkawa ke kara nuna rashin gamsuwa da salon tafiyar da gwamnatin kasarsu.

Manyan dalilan da suka haddasa hakan a cewar cibiyar, sun hada da gazawar gwamnatin Amurka a fannin yaki da annobar COVID-19, da tsanantar yanayin siyasar kasar, da fadadar gibi tsakanin talakawa da mawadata, da wariyar launin fata. Rahoton ya kuma nuna yiwuwar Amurkawa su ci gaba da nuna rashin gamsuwa da salon gwamnatinsu.

Ko shakka babu, samun amincewar al’umma shi ne ginshikin bunkasuwa da ci gaban ko wace kasa. To sai dai kuma ga alama ‘yan siyasar Amurka na fuskantar kalubalen rashin samun karbuwa daga al’umma, don haka lokaci ne na farkawa daga barci!  (Saminu)