Xi: Ya dace kasashen duniya su hada kai don yakar kalubaloli masu tsanani dake gabansu
2022-01-19 09:34:39 CRI
A ranar Litinin 17 ga watan Janairun shekarar 2022 ne, shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya gabatar da jawabi ga taron tattalin arziki na duniya na Davos ta kafar bidiyo, inda ya ce kasashe daban daban na da damar samun ci gaba tare, idan sun martaba junan su, sun kuma nemi hanyar samun moriya daga juna, ta hanyar jingine banbance banbancen dake tsakaninsu.
Shugaba Xi ya ce, hanya mafi dacewa da bunkasa rayuwar dan Adam ita ce, samar da ci gaba cikin lumana da hadin gwiwar cimma moriyar juna. Ya kuma yi kira ga kasashen duniya da su lura da irin abubuwan da suka wakana a tarihi, su yi kokarin samar da daidaito ga dokokin kasa da kasa, su yayata ka’idojin ciyar da bil adama gaba, tare da gini al’umma mai makomar bai daya ga dukkanin bil adama.
Ya kuma bukaci kasashen duniya da su zabi hawa teburin shawara maimakon yin fito na fito, su hade kai maimakon warewa, su kuma rungumi dukkanin hanyoyin hadin kai, su yi watsi da kariyar cinikayya, da danniya ko nuna karfi a siyasance.
Har ila yau, shugaban na Sin ya ce, ba burin kasar sa ba ne wanzar da daidaito kadai, domin kuwa a matakin farko akwai bukatar fadada gajiya, sannan a rarraba ta yadda ya kamata, ta hanyar tsarin aikin hukumomi masu ruwa da tsaki. Shugaba Xi ya ce Sin za ta ci gaba da aiwatar da matakan kare muhalli.
Xi Jinping ya bayyana kwarin gwiwar sa, game da shirin kasar Sin na gudanar da gasar Olympic da ajin gasar na nakasassu dake tafe a birnin Beijing, cikin kyakkyawan yanayin tsaron lafiya.
Taken gasar Olympic ta birnin Beijing ta 2022 shi ne, "Aiki tare domin makomar bai daya ga bil adama." (Saminu, Ibrahim/Sanusi Chen)