Gasar Wasanni Taro Ne Na Hadin Kai
2022-01-19 19:19:16 CRI
Yayin da kasar Sin ta shirya tsaf don fara gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing a ranar 4 ga watan Fabrairun shekarar 2022, ana can kuma ana fafatawa a gasar cin kofin kwallon kafan kasashen nahiyar Afirka (AFCON) a kasar Kamaru.
Saboda muhimmancin wasannin, ya sa gwamnatin kasar Kamaru ta rage lokutan tashi a ma’aikatu da makarantu, don baiwa jama’a damar kallon wasannin dake gudana, baya ga samar musu da motocin bas-bas da za su rika kai su filayen wasan, kana a dawo da su gidajensu bayan kammala wasannin kyauta. Wannan ya kara tabbatar da muhimmancin wasanni ga ci gaba da ma hadin kan daukacin bil-Adama.
A kasar Sin kuma, yanzu haka, masu shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi da zai gudana a nan birnin Beijing, sun gabatar da tsarin karshe da ya shafi manufofin 'yan kallo na gasar wasannin.
Wannan ya shaida cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing, gagarumin biki ne ga ’yan wasa da za su halarci gasar da masu sha’awar wasan a fadin duniya, inda suke zumudin ganin an gudanar da gasar kamar yadda aka tsara. Mahukuntan kasar Sin sun sha nanata cewa, za a shirya gasa mai kayatarwa da za ta gamsar da duniya a dukkan fannoni.
Masu fashin baki na kara jaddada cewa, gasar wasannin kamar Olympics da AFCON da sauran wasanni dangin wadannan, za su sa kaimi ga hadin gwiwa tare da samar da fata ga daukacin bil-adama.
Don haka, ana fatan dukkan kasashe su yi biyayya ga kudurin ruhin Olympics, da sauran wasanni, domin siyasantar da harkar wasanni, babu abin da zai haifar, illa rarrabuwar kawuna da koma baya. Gasar wasanni, wani taro ne na zaman lafiya da hadin kai, ba kuma dandali ne na neman cimma moriyar siyasa ba.
Saboda muhimmancin wannan gasa, shugabannin kasashen duniya da dama sun bayyana fata da kuma goyon bayansu ga gasar Olympics ta Beijing dake tafe. Babban sakataren MDD Antonio Guterres, da shugaba Putin na Rasha da sauran shugabannin duniya, sun sanar da cewa, za su halarci bikin bude gasar a nan birnin Beijing.
Gudanar da wannan gasa a birnin Beijing, wanda ke zama birni daya tilo a duniya da ya shirya gasar wasannin Olympics na zafi da lokacin hunturu, zai kara bunkasa harkokin wasannin a kasar Sin. (Ibrahim Yaya)