logo

HAUSA

Jami’ar Zimbabwe na sa ran ganin an shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Beijing cikin nasara

2022-01-19 14:26:51 CRI

Jami’ar Zimbabwe na sa ran ganin an shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Beijing cikin nasara_fororder___172.100.100.3_temp_9500033_1_9500033_1_1_ad81ef77-f1b1-4ea8-b042-3e8fdca0d18e.JPG

Jiya ne, mambar kwamitin wasannin Olympics na duniya kuma ministar matasa da wasannin motsa jiki ta kasar Zimbabwe Kirsty Coventry, ta zanta da wakilin babban gidan rediyo da talibijin na kasar Sin na CMG, inda ta yi imanin cewa, gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta shekarar 2022 da za a yi a Beijing, za ta kasance wata gagarumar gasar, tana sa ran ganin an gudanar da gasar cikin nasara.

“Beijing birni ne da ba zan taba mantawa a zuciyata ba. Na lashe lambar zinare daya da azurfa guda uku a Beijing. Sabo da na halarci gasar wasannin Olympics ta shekarar 2008 da aka yi a Beijing, don haka na yi imani da alkawarin kasar Sin na shirya gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi mai kayatarwa. Hakika na yi farin ciki sake komawa Beijing don shaida wannan gasa.” (Kande Gao)