logo

HAUSA

Gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Beijing ta shaida alkawarin da Sin ta yi na martaba ruhin Olympic

2022-01-19 14:25:24 CRI

Gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Beijing ta shaida alkawarin da Sin ta yi na martaba ruhin Olympic_fororder_希腊

Kasar Sin ta cika alkawarin da ta yi na martaba ruhin Olympic, ta hanyar shiryar gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu. Shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na kasar Girki Spyros Capralosm shi ne ya fadi haka, yayin da yake zantawa da wakilin kamfanin dillancin labarai na kasar Sin na Xinhua a kwanan nan.

Spyros ya yaba da yadda kwamitin kula da wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing ya dauki tsauraran matakan rigakafin yaduwar cutar COVID-19. Ya kuma yi imanin cewa, tabbas kasar Sin za ta samu nasarar shirya gasar.

Haka kuma Capralos ya ce, ta hanyar shirya gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu ta Beijing, za a ci gaba da nuna aniyar bil Adama ta haye wahalhalu. Yana mai cewa, dole ne ’yan wasa da masu yi musu rakiya, su martaba tsauraran matakan rigakafin cutar da aka tsara na gudanar gasar. A cewarsa, “Kasar Sin na tsara dimbin ayyuka don tinkarar matsaloli daban daban da ka iya kunno kai.”

Bugu da kari, Capralos na ganin cewa, gasar za ta kasance daya daga cikin gasannin wasannin Olympics da suka fi dora muhimmanci kan kiyaye muhalli. Ya kuma ba da misalin cewa, yadda aka sake amfani da wasu dakunan wasanni na gasar wasannin Olympcis na lokacin zafi ta shekarar 2008 ya burge shi sosai. (Kande Gao)