logo

HAUSA

Kasar Sin na fatan ayyukan ICC za su wanzar da zaman lafiya mai dorewa a Dafur na Sudan

2022-01-18 11:26:28 CRI

Kasar Sin na fatan ayyukan ICC za su wanzar da zaman lafiya mai dorewa a Dafur na Sudan_fororder_220118-f02-ICC

Mataimakin zaunannen wakilin kasar Sin a MDD Geng Shuang, ya bayyana fatan kasarsa na ganin ayyukan kotun hukunta manyan laifuffuka ta kasa da kasa ICC, sun kai ga cimma zaman lafiya da tsaro mai dorewa a yankin Dafur na Sudan.

Geng Shuang ya shaidawa Kwamitin Sulhu na MDD cewa, ya kamata kotun ICC ta kiyaye ka’ida kasancewar batun na gaban shari’a, kana ta martaba cikakken ’yancin da tsarin shari’ar kasar ke da shi. Haka kuma Sin na fatan ayyukan kotun bisa kudure-kuduren kwamitin Sulhu na MDD, za su kai ga cimma zaman lafiya da tsaro mai dorewa a yankin Dafur.

Ya kara da cewa, Sin na bibiyar yadda ICC ke tafiyar da batutuwan da suka shafi Sudan, kuma tana sane da irin ayyukan da babban mai shigar da kara na kotun wato Karim Khan ya yi tun bayan da ya kama aiki.

Ya ce bisa la’akari da rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta Juba, Dafur ya shiga wani sabon mataki na wanzuwar zaman lafiya. Kuma kasar Sin na karfafawa dukkan masu ruwa da tsaki gwiwar ci gaba da aiwatar da kunshin yarjejeniyar, kana tana kira ga bangarorin Dafur da ba su rattaba hannu ba, su gaggauta shiga a dama da su cikin shirin na wanzar da zaman lafiya. (Fa’iza Mustapha)