logo

HAUSA

An kammala manufofin 'yan kallo na Beijing 2022

2022-01-18 10:34:08 CRI

An kammala manufofin 'yan kallo na Beijing 2022_fororder_220118-i01-Beijing 2022 spectator policy finalized

Jiya ne, masu shirya wasannin Olympics na lokacin sanyi da zai gudana a nan birnin Beijing, suka gabatar da tsarin karshe da ya shafi manufofin 'yan kallo na gasar wasannin.

Wata sanarwa da mashirya gasar suka fitar ta bayyana cewa, bisa la'akari da halin da ake ciki a halin yanzu, da kuma yanayi mai sarkakiya game da cutar COVID-19, da tabbatar da tsaron dukkan mahalarta da masu kallo, an yanke shawarar cewa, ba za a sake sayar da tikitin gasar ba, amma a kasance cikin shirin da aka daidaita wanda zai gayyaci kungiyoyin 'yan kallo su kasance a wurin a lokacin wasannin.

Sanarwar ta kara da cewa, a ranar 30 ga watan Satumban shekarar 2021 ne, aka fitar da ka'idojin rigakafin kamuwa da COVID-19 na wasannin Oympics na Beijing 2022. Daya daga cikin ka'idojin shi ne cewa, ba za a sayar da tikiti ga 'yan kallo daga wajen babban yankin kasar Sin ba. Amma za a sayarwa ’yan kallo daga babban yankin da suka cika ka’idojin matakan rigakafin COVID-19.

Za a gudanar da gasar wasannin Olympics na lokacin sanyi na Beijing daga ranar 4 zuwa 20 ga watan Fabrairu, yayin da kuma za a gudanar da gasar wasannin ajin nakasassu daga ranar 4 zuwa 13 ga Maris na shekarar 2022 da muke ciki. (Ibrahim)