logo

HAUSA

Ana sa rana samun tururwar matafiya yayin bikin bazara na kasar Sin

2022-01-18 10:04:47 CRI

Ana sa rana samun tururwar matafiya yayin bikin bazara na kasar Sin_fororder_220118-f01-China Spring Festival

Ma’aikatar kula da zirga-zirga ta kasar Sin, ta ce ana sa ran ganin tafiye-tafiyen da yawansu zai kai biliyan 1.18, yayin bikin bazara na kasar Sin na bana. Adadin da ya karu da kaso 35.6 a kan na bara, kana ya yi kasa da kaso 20.3 idan aka kwatanta da na 2020.

Lokacin tafiye-tafiyen da zai shafe kwanaki 40 da ake kira da Chunyun, ya fara ne tun daga jiya Litinin, inda jama’a za su yi bulaguro domin haduwa da iyalansu da murnar sabuwar shekarar gargajiya ta kasar da ake kira Bikin Bazara, wanda a bana ya fado a ranar 1 ga watan Fabreru.

Tashoshin jiragen kasa da na sama, sun matse kaimi wajen kandagarkin annobar COVID-19, ciki har da inganta hidimomin da babu ma’amala ta kai tsaye da kara feshin kashe kwayoyin cuta da auna zafin jiki. (Fa’iza Mustapha)