logo

HAUSA

Schwab: Tattaunawa da hadin gwiwa su ne muhimman hanyoyin kyautata zaman lafiya da ci gaban bil adama

2022-01-18 11:38:02 CRI

Schwab: Tattaunawa da hadin gwiwa su ne muhimman hanyoyin kyautata zaman lafiya da ci gaban bil adama_fororder_220118-a01-Schwab

Klaus Schwab, shugaban dandalin raya tattalin arzikin duniya WEF, ya ce, tattaunawa da yin hadi gwiwa su ne muhimman hanyoyin dake jagoranci wajen lalibo bakin zaren tabbatar da zaman lafiya da kyautata zaman rayuwar bil adama, Klaus ya bayyana hakan ne a taron WEF na shekarar 2022 ta kafar bidiyo.

Schwab ya ce, “Tilas ne mu hada dukkan karfinmu wajen samun alaka mai karfi, da shigar da kowane bangare, da kuma samar da karin bunkasuwar tattalin arzikin duniya mai dorewa." Ya kara da cewa, shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da muhimmin jawabi a taron mai taken “Kwarin gwiwa don dorawa zuwa mataki na gaba domin yin hadin gwiwa don samar da kyakkyawan yanayin duniya bayan kawo karshen annobar COVID-19 a duniya”.

Gabanin jawabin shugaba Xi, Schwab ya yaba wa nasarorin da kasar Sin ta samu wajen gina al’umma mai matsakaiciyar wadata daga dukkan fannoni. Ya nuna cewa kasar Sin ta cimma nasarar kafa muhimmin tarihi.

Da yake bayani game da kalubalolin dake tinkarar bil adama, ya bayyana cewa, wannan shi ne lokaci mafi dacewa da ya kamata shugabanni su hada kansu don yin aiki tare domin shigar da kowane bangare na duniya, da samar da karin ci gaba mai dorewa, da kuma karin ci gaban duniya.

A jawabinsa, Schwab ya yiwa kasar Sin fatan samun cikakkiyar nasarar karbar bakuncin gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu dake tafe. (Ahmad Fagam)