logo

HAUSA

Masanin Morroco: Saurin ci gaban kasar Sin ya sa ake Allah Allah da gasar wasannin Olympics da ke tafe

2022-01-18 14:08:54 CRI

Masanin Morroco: Saurin ci gaban kasar Sin ya sa ake Allah Allah da gasar wasannin Olympics da ke tafe_fororder_0d338744ebf81a4c03d6dc9be04ade50242da661

Kwanan nan, a yayin da yake amsa tambayoyin da wakilin kafar APP ta jaridar Beijing Daily ya yi masa, shugaban kungiyar kula da hadin gwiwa da ci gaba tsakanin Sin da kasashen Afirka ta kasar Morroco, Nasser BOUCHIBA ya bayyana cewa, sakamakon saurin ci gaban kasar Sin da ma gaggaruman nasarorin da aka samu a gasar wasannin Olympics da aka gudanar a shekarar 2008 a birnin Beijing, shi ya sa ake allah allah da gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu da za a bude nan ba da jimawa ba. Ya ce, tabbas kasar Sin za ta gudanar da gasar mai kayatarwa matuka. Morroco ta kasance kasa ta farko daga cikin kasashen arewacin Afirka, wadda ta kulla yarjejeniyar hadin gwiwar aiwatar da shawarar ziri daya da hanya daya, wadda ta dace da bukatun ci gaban kasar, kuma hadin gwiwar kasashen biyu zai zama abin koyi ga hadin gwiwar Sin da kasashen Afirka a nan gaba. (Lubabatu)