Nacewa sabanin ra’ayi ka iya tsananta yanayin da duniya ke ciki
2022-01-18 16:44:02 CRI
A jiya Litinin ne aka bude taron tattalin arziki na kasa da kasa, wato DAVOS, inda shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar da jawabi. Kuma a cikin jawabin nasa, ya tabo batutuwa masu muhimmanci dake kawo tarnaki ga ci gaban tattalin arzikin duniya har ma da al’umma baki daya.
Daga cikin batutuwan, ya tabo yadda kasashe daban-daban ke da damar samun ci gaba idan suka hada hannu. Har kullum, shugaban kasar Sin kan yi kira ga huldar kasa da kasa da kyautata yanayin duniya. Hakika akwai dimbin damarmaki ga kasashen duniya wajen raya kansu idan har za su ajiye sabanin dake akwai. Lallai shaidu sun riga sun nuna cewa, ba za a samu ci gaba ba, muddun aka tsaya kan fito na fito da neman kakaba tsari ko ra’ayin wata kasa kan wata. Kasancewar al’ummu daga kasashe daban-daban da yankuna, dole ne a samu bambancin tunani da al’ada a tsakaninsu, amma abu mafi muhimmanci shi ne, yadda za a girmama wadannan bambance-bambance da samun daidaito mafi karbuwa ga kowa domin a gudu tare a tsira tare. Abun da zaman lafiya bai kawo ba, rashinsa ba zai taba kawowa ba. Tsamin dangantaka tsakanin kasashen duniya zai iya haifar da bala’in da ya haura wanda ake ciki yanzu. Don haka ya dace manyan kasashe su gane hakan, domin duk wata fitina da suke kokarin tadawa, su ma zai shafe su. Misali, an ga yadda ’yan kasuwannin Amurka suka yi ta kokawa dangane da yadda suke dandana kodarsu saboda harajin da kasarsu ta kakabawa kayayyakin Sin.
Yayin da ake ta kiraye-kirayen kiyaye muhalli da halittu, shugaban na Sin ya ce, Sin ba za ta cimma burinta na ci gaba ta hanyar gurgunta albarkatu ko muhalli ko yanayi ba. Batun gurbatar muhalli da yanayi abu ne dake daukar hankalin duniya, haka kuma batun neman ci gaba. Duk da burinta na neman ci gaba, kasar Sin tana kokarin kare muhalli. Bai kamata neman ci gaba ya rufe idon gwamnatoci ta yadda har za su manta kiyaye muhalli ba. Muhalli da halittu ciki har da bil adama, abubuwa ne da ba za a taba raba su da juna ba, don haka, dole ne duk wani nau’i na ci gaba, ya yi la’akari da kare muhalli domin kyautata rayuwar bil adaman da ake neman ci gaban dominsu, domin idan babu su, ci gaban ba zai yi tasiri ba.
Har wa yau, ya tabo yadda tattalin arzikin kasar Sin ke cikin kyakkyawan yanayi, inda har karuwar alkaluman GDPn ya kai kaso 8 bisa dari. Kamar kowacce kasa, Sin ta fuskanci mummunan tasirin COVID-19 a kan tattalin arzikinta. Sai dai kuma, managartan matakanta sun taimaka gaya wajen shawo kan annobar tare da farfado da tattalin arzikinta. Tubalin tattalin arzikin kasar na da karfi, haka kuma tana da juriya. Yadda Sin ta mayar da hankali wajen raya tattalin arzikinta a cikin gida da kuma jajircewar shugabanninta, ya taimaka gaya wajen farfado da tattalin arzikinta.
Akwai dimbin darussa da kasashen duniya za su iya dauka daga jawabin na shugaban kasar Sin da ma matakai da gogewarta domin ganin tattalin arzikin duniya ta farfado har ma da kai wa matsayin da ake fata. (Faiza Muhammad Mustapha)