logo

HAUSA

Mafarkin marigayi Martin Luther King bai tabbata ba sama da shekaru 50 da bayyana shi

2022-01-18 21:48:34 CRI

Mafarkin marigayi Martin Luther King bai tabbata ba sama da shekaru 50 da bayyana shi_fororder_b64543a98226cffc1b06797df226f799f703ea86

“Na yi mafarki cewa, wata rana wannan kasa za ta daga zuwa matsayi na hakika daidai da kimarta: ‘Mun yi imani wannan gaskiya ce a zahiri, cewa dukkanin dan Adama matsayin sa daya’. Na yi mafarki cewa, wata rana can a saman tsaunukan Georgia, dan tsohon bawa da dan tsohon mai mallakar bayi, za su zauna kan tebur guda a matsayin ‘yan uwa. Na yi mafarki cewa, wata rana, jihar Mississippi, jiha mai cike da rashin adalci, mai cike da danniya, za ta sauya zuwa dausayi na ‘yanci da adalci. Na yi mafarki cewa, wata rana ’ya’ya na kanana su 4, za su rayu a kasa da ba za a rika kallon launin fatar su ba, maimakon haka, za a rika kallonsu bisa dabi’un da suke da su……”

Yau sama da shekaru 50 da suka wuce, marigayi Martin Luther King, jagoran fafutukar kare ‘yancin bakaken fata na kasar Amurka, ya bayyana a jawabinsa, yadda Amurkawa bakaken fata ke matukar fatan ganin an tabbatar da ‘yanci da adalci gare su, kuma har zuwa yanzu, ta kalamansa ne muke iya ganin yadda wannan kyakkyawan mafarkinsa ya kasance, wato a kawar da kabilanci kwata kwata, yadda al’ummu za su iya zaman daidaito da juna duk da bambancin launin fatansu da al’adunsu da addinansu.

Mafarkin marigayi Martin Luther King bai tabbata ba sama da shekaru 50 da bayyana shi_fororder_b2de9c82d158ccbf532af05422460337b0354175

A jiya ne aka gudanar da harkoki na tunawa da ranar Martin Luther King karo na 27 a kasar Amurka, inda dubun dubatar al’ummun kasar suka shiga ayyukan sa kai, don tunawa da marigayin, wanda ya ba da babbar gudummawa wajen kare ‘yancin al’ummar kasar Amurka.

Sai dai a yayin da Amurka ke bayyana imanin ta kan ‘yanci da adalci bisa sunan Martin Luther King, ko mafarkin marigayin ya tabbata bayan ya bayyana shi a shekaru sama da 50 da suka wuce?

Rahoton yanayin tattalin arziki na iyalan kasar Amurka a shekarar 2020 da hukumar Fed ta kasar Amurka ta fitar a bara ya yi nuni da cewa, a zahiri dai, Amurkawa ‘yan asalin Afirka a baya suke, idan an yi nazari a kan yanayin da suke ciki ta fannonin kudin shiga, da gidajen zama, da rancen kudin da bankuna ke samar musu, da samun aikin yi, da ilmantarwa da sauransu, da ma yanayin da fararen fata ke ciki.

Misali ta fannin kudin shigar iyali, kudin da kimanin kaso 41% na iyalan Amurkawa ‘yan asalin Afirka ke samu bai kai dalar Amurka dubu 25 ba a kowace shekara, a yayin da wannan adadi bai wuce kaso 21% ba kacal ga fararen fata.

Mafarkin marigayi Martin Luther King bai tabbata ba sama da shekaru 50 da bayyana shi_fororder_9922720e0cf3d7ca892d0a5399445a0f6a63a99a

Kabilanci ya kuma haifar da tasiri ga sassan shari’a. Idan ba a manta ba, a ranar 25 ga watan Mayun shekarar 2020, dan sandan Amurka farar fata Derek Chauvin ya kashe George Floyd, ba’amurke dan asalin Afirka, kuma yadda George Floyd ya ce “na kasa numfashi” ya sake shaida matsalar kabilanci da ta dade tana addabar kasar ta Amurka. Alkaluman wani shiri mai zaman kansa na Amurka mai lakabin “Taswirar bayyana yadda ‘yan sanda suka nuna karfin tuwo” sun nuna cewa, a shekarar 2020, mutane 1,126 da ‘yan sanda suka kashe a Amurka, kaso 28 cikin 100 ‘yan asalin Afirka ne.

Shekaru sama da 150 ke nan da aka yi watsi da tsarin mallakar bayi a kasar Amurka, kuma shekaru sama da 50 bayan da marigayi Martin Luther King ya bayyana mafarkin Amurkawa bakaken fata, na tabbatar da ‘yanci da adalci a gare su, amma har yanzu a kasar Amurka, zaman daidaito a tsakanin kowa ya kasance wani mafarki ga ‘yan kasar bakaken fata, kuma hakan ya faru ne sakamakon irin mummunan ra’ayi na kabilanci da ya shiga jinin kasar tun farkon fari, kuma tuni wannan ra’ayi na “fararen fata sun fi saura” ya zauna da gindinsa a kasar.

A yayin da ake tunawa da marigayi Martin Luther King a kasar, tambaya ita ce, shin ya yiwu mafarkinsa ya tabbata? (Lubabatu)