logo

HAUSA

Muryar Sin ta amsa tambayoyin da duniya ke da su a yau

2022-01-18 19:04:08 CRI

Muryar Sin ta amsa tambayoyin da duniya ke da su a yau_fororder_WEF

Shugaban taron tattalin arziki na duniya Klaus Schwab, ya ce jawabin da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gabatar, a yayin taron WEF na bana, ya zama wani jigo na bunkasa hadin gwiwar kasa da kasa. Schwab ya ce jawabin ya nunawa duniya yiwuwar samun ci gaba mai ma’ana cikin shekaru masu zuwa.

A jiya Litinin 17 ga watan nan ne, shugaba Xi Jinping ya halarci taron tattalin arziki na WEF na bana ta kafar bidiyo, inda ya gabatar da jawabin sa daga nan birnin Beijing.

Jawabin na shugaba Xi ya zamo aikin diflomasiyyar kasa da kasa na farko da ya gudanar a sabuwar shekarar nan, kuma kamar yadda aka saba a tarihi, ya gabatar da shawarwari, tare da bayyana wasu manufofi 3, wadanda za su taimaka wajen shawo kan manyan kalubalen da duniya ke fuskanta, wanda hakan ya nunawa duniya a fili kwazon Sin, da himmarta ta ingiza hadin gwiwar kasa da kasa. (Saminu)