logo

HAUSA

Jami’an kasar Afirka ta kudu sun bayyana fatan alheri ga gasar wasannin Olympics da ke tafe

2022-01-18 11:15:27 CRI

Jami’an kasar Afirka ta kudu sun bayyana fatan alheri ga gasar wasannin Olympics da ke tafe_fororder_W020211214217261105104

A jiya Litinin, karamin ofishin jakadancin kasar Sin da ke birnin Cape Town na kasar Afirka ta Kudu, ya wallafa wani shirin bidiyo na yayata gasar wasannin Olympics da za a bude nan ba da jimawa ba, inda shugaban kwamitin kula da wasannin Olympics na kasar ta Afirka ta kudu da mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar suka bayyana fatan alheri ga gasar.

Barry Hendricks, shugaban hadaddiyar kungiyar wasanni ta kasar Afirka ta kudu kana shugaban kwamitin shirya gasar wasannin Olympics na kasar ya bayyana cikin shirin cewa, “Ina mika fatan alheri ga kwamitin shirya wasannin Olympics na lokacin hunturu na birnin Beijing. Ina fatan kome ya tafi daidai kamar yadda aka tsara bisa kokarin da kuke yi. Ina kuma da imanin cewa, tabbas za ku cimma nasarar gudanar da gasar da za ta burge kowa.”

Solomon Tsenoli, mataimakin shugaban majalisar dokokin kasar Afirka ta kudu ya ce, wasannin Olympics na lokacin hunturu za su taimaka ga karfafa hadin kan al’ummun kasashen duniya, ya kuma yi fatan za a gudanar da gasar cikin nasara.

Shi ma karamin ofishin jakadancin kasar Sin da ke birnin Cape Town, ya bayyana fatansa na ganin shirin ya taimaka ga yayata gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu tsakanin bangarori daban daban na kasar Afirka ta kudu, tare da isar da fatan alheri ga gasar. (Lubabatu)