Beijing Olympics 2022: Kasashen Duniya Na Adawa Da Siyasantar Da Gasar Olympics
2022-01-17 17:20:33 CRI
Yayin da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing 2022 ke karatowa, shugabannin kasashen duniya da dama suna ci gaba da bayyana fatansu na ganin kasar Sin ta karbi bakuncin gasar wasannin cikin nasara, a hannu guda kuma, suna nuna adawa da siyasantar da gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing. Wanzar da zaman lafiya, karfafa zumunci, kyautata alaka, da kuma tabbatar da hadin kan al’ummun kasashen duniya na daga cikin muhimman manufofin shirya wasannin. Kamar yadda ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayyana a karshen mako cewa, gasar wasannin Olympics ta lokacin sanyi ta Beijing za ta sa kaimi ga hadin gwiwa tare da samar da fata ga daukacin bil-adama. Ana fatan dukkan kasashe za su yi biyayya ga kudurin ruhin Olympics. Mai magana da yawun ma’aikatar Wang Wenbin, ya yi tsokaci game da rahotannin shirin Amurka na shirya ayyukan horas da sojoji tare da kawayenta a yankunan da ke makwabtaka da kasar Sin a lokacin wasannin. Sai dai wannan aniyar ta Amurkar na shan suka daga bangarorin kasa da kasa. Ya zuwa yanzu, shugabannin kasashen duniya da dama sun bayyana kyakkyawan fatansu da kuma nuna goyon bayan gasar Olympics din dake tafe. Alal misali, firaministan kasar Pakistan Imran Khan, da babban sakataren MDD Antonio Guterres, duk sun sanar cewa, za su halarci bikin bude gasar a birnin Beijing. Ita mai kasar Mali tana maraba da kasar Sin na karbar bakuncin gasar wasannin Olympics na lokacin hunturu na Beijing 2022, kamar yadda kakakin gwamnatin rikon kwaryar kasar, Abdoulaye Maiga, ya bayyana cikin wata sanarwa a karshen mako. Maiga ya ce, za a gudanar da gasar wasannin Olympic ta lokacin sanyi karo na 24 a daidai lokacin da ake fama da kalubalen kiwon lafiya sakamakon barkewar annobar COVID-19. Sai dai duk da irin yanayin da ake ciki, wasannin za su ci gaba da kiyaye ruhin karfafa zumunta da alaka a tsakanin kasashen duniya wanda ya yi daidai da manufar ruhin shirya wasannin Olympic wanda bai taba lamintar siyasantar da harkar wasannin ba. Haka zalika, rahoton da jaridar Herald ta kasar Zimbabwe ta wallafa a karshen mako ta bayyana cewa, ministar yada labaran kasar Zimbabwe, Monica Mutsvangwa, ta bayyana cewa, gwamnatin kasar ta ba da cikakken goyon bayanta ga gasar wasannin motsa jiki ta lokacin hunturu ta Beijing ta shekarar 2022, kana tana adawa da yunkurin siyasantar da gasar wasannin ta Olympics da wasu kasashe ke yi. Zimbabwe tana yiwa kasar Sin fatan samun cikakkiyar nasarar karbar bakuncin gasar wasannin Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing. Jami’an kasashen Afirka da dama sun nuna goyon baya kan gasar Olympics ta lokacin hunturu ta Beijing. A karshen makon da ya gabata, shugaban kasar Comoros Azali Assoumani, ya bayyana cewa, ko da yake, ana fuskantar matsalar yaduwar annobar cutar numfashi ta COVID-19, amma, tabbas ne, kasar Sin za ta cimma nasarar gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics ta lokacin hunturu, za ta kuma tabbatar da tsaron lafiyar ‘yan wasan kasashen duniya, da ma jama’ar kasar Sin yadda ya kamata. Haka dai jami’ai da masana da shugabanni da dama daga sassan duniya ke bayyana ra’ayoyinsu game da wannan muhimmiyar gasar wanda kasar Sin zata karbi bakuncinta a watan gobe, da fatan kwalliya zata biya kudin sabulu. (Ahmad Fagam)