logo

HAUSA

GDPn Sin ya karu da kaso 8.1 bisa dari a shekarar 2021

2022-01-17 19:14:46 CRI

GDPn Sin ya karu da kaso 8.1 bisa dari a shekarar 2021_fororder_GDP

Kafin shekara daya da ta gabata, kasar Sin ta taka babbar rawa kan karuwar tattalin arzikin duniya. A wancan lokaci, kamfanin dillancin labarai na Bloomberg News na Amurka, ya taba gabatar da rahoton cewa, karuwar tattalin arzikin kasar Sin tana sa kaimi kan farfadowar tattalin arzikin duniya, a yanzu kuwa, an fitar da alkaluman tattalin arzikin shekarar 2021, inda aka tabbatar da gudummowar kasar Sin kan farfadowar tattalin arzikin duniya.

Yau Litinin, hukumar kididdigar kasar Sin ta fitar da alkaluman tattalin arzikin kasar, inda aka bayyana cewa, tattalin arzikin kasar Sin yana ci gaba da samun bunkasuwa a shekarar da ta gabata, wato gaba daya adadin GDPn kasar ya kai kudin Sin Yuan triliyan 114.4, adadin da ya kai matsayi na biyu a fadin duniya, kuma ya karu da kaso 8.1 bisa dari idan aka kwatanta da makamancin lokacin shekarar 2020.

Kana hukumar kididdigar kasar Sin ta bayyana cewa, an yi hasashen cewa, gudummowar da kasar Sin ta baiwa karuwar tattalin arzikin duniya a bara, za ta kai kaso 25 bisa dari.

Abu mafi muhimmanci shi ne, kayayyakin kiwon lafiyar da kasar Sin ta samar, sun taka babbar rawa wajen dakile yaduwar annobar cutar COVID-19 a fadin duniya, inda ya zuwa karshen bara, gaba daya, kasar Sin ta gabatarwa sauran kasashen duniya marufin baki da hanci biliyan 372, da kayan ba da kariya biliyan 4.2, da sinadarin tantance kwayar cutar biliyan ga mutane 8.4. Haka zalika, kasar Sin samar da alluran rigakafi sama da biliyan 2 ga kasashe da kungiyoyin kasa da kasa fiye da 120, inda har ta kasance kasa wadda take samarwa ketare alluran mafi yawa a duniya.(Jamila)