logo

HAUSA

Xi: Dukkanin bil Adama za su samu makoma mai haske

2022-01-17 20:46:29 CRI

Xi: Dukkanin bil Adama za su samu makoma mai haske_fororder_hoto

A yau Litinin ne shugaban kasar Sin Xi Jinping, ya halarci taron dandalin tattalin arzikin kasa da kasa (WEF) na shekarar 2022 ta kafar bidiyo, inda ya kuma ba da jawabi.

Cikin jawabinsa, shugaba Xi ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasashen duniya suna fuskantar da sauye-sauyen da ba a taba ganin irin su ba, kuma, ba kawai suna shafar wata kasa ko wani yanki ba ne, sauye-sauye ne dake shafar dukkanin mu. Ya ce ya kamata mu nemi ci gaba bisa halin da muke ciki.

Ya kuma jaddada cewa, abubuwan da suka faru sun nuna mana cewa, a halin yanzu, dukkanin kasashen duniya suna cikin babban jirgin ruwa guda daya, don haka ya kamata mu hada kanmu, domin fuskantar kalubalolin dake gabanmu.

Haka zalika kuma, ya ce, “Za mu ci gaba da samun dunkulewar tattalin arziki, don haka ya kamata kasa da kasa su tsaya tsayin daka wajen goyon bayan manufar cude-ni-in-cude-ka, da kara bude kofa ga waje, da karfafa hadin gwiwa, domin kafa wani tsarin tattalin arziki mai bude kofa ga waje tsakanin kasashen duniya”. (Mai Fassarawa: Maryam Yang)